SHEKARANJIYA, 26 ga Nuwamba, 2021, aka ɗaura auren jarumar Kannywood Maryam Musa Waziri da sahibin ta, tsohon fitaccen ɗan ƙwallon ƙafa na ƙungiyar ‘Green Eagles’ ɗin nan Tijjani Babangida.
An ɗaura auren a Kaltungo, Jihar Bauchi.
A ranar Alhamis, Maryam ta wallafa wani bidiyon ta a Instagram a cikin shigar amarci, ta na bayyana farin ciki da sabon yanayin da ta shiga.
Ta kuma yi addu’ar samun kariya daga Ubangiji game da wannan aure da ta yi.
A bidiyon akwai muryoyin mata masu taya ta murna, har da guɗa.
Angon jarumar haifaffen garin Kaduna ne, kuma shekarun sa 48.

Bayan wasan da ya yi wa Eagles, Tijjani Babangida ya kuma buga wa ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na ƙasar waje wasa, musamnan ma Ajax ta ƙasar Nezalan da Al-Ittihad ta Saudi Arebiya.
Angon yanzu ya yi ritaya daga buga ƙwallo, sai dai ɗan kasuwa ne kuma ejan na harkar ƙwallo.
Tijjani ya taɓa auren wata Balarabiyar ƙasar Tunisiya mai suna Rabah, wadda ƙanwa ce ga matar shahararren ɗan ƙwallon nan Daniel Amokachi. Amma yanzu sun rabu.

Babu cikakken bayani game da auren Tijjani da Maryam Waziri, amma wata majiya ta shaida wa mujallar Fim cewa amaryar ta tare a gidan mijin ta a Kaduna.
Ɗimbin masoya sun taya ma’auratan murna a soshiyal midiya.
Mu ma mu na addu’ar Allah ya ba su zaman lafiya da ƙaruwar arziki, amin.


