TA faru ta ƙare. A yau Juma’a, 16 ga Yuni, 2023 aka ɗaura auren mawaƙin gambara, Abubakar Ibrahim, wanda aka fi sani da G-Fresh Al-Ameen ko Kano State Material, da tsohuwar jaruma kuma furodusa a Kannywood, Sayyada Sadiya Haruna.
An ɗaura auren nasu da misalin ƙarfe 2:00 na rana bayan sallar Juma’a a Masallacin Sheikh Isyaka Rabi’u da ke Goron Dutse cikin birnin Kano, a kan sadaki N200,000.

Da alama amarya Sadiya ta ƙagu a ɗaura auren, domin kuwa ta yi bidiyo a cikin mota inda ta kira ango a waya ta na tambayar sa idan an ɗaura, shi kuma ya ba ta amsa da cewa an dai kusa, ya ce waliyai sun taru.
Da ya ke dukkan su sun shahara a soshiyal midiya, babu wanda bai san da soyayyar su ba, duk da yake ba a ɗauki tsawon lokaci da fara ta ba.
A kwanan baya sun samu matsala, wanda har ake tunanin maganar auren su ta wargaje, sai daga baya kuma su ka shirya, har ta kai ga sun zama ɗaya a yau.

Sadiya dai ta shahara wajen sayar da kayan ƙarin ni’imar aure da na ƙarfin maza ta hanyar soshiyal midiya, yayin da shi kuma angon mawaƙin gambara ne, inda ya yi shuhura da waƙar sa mai taken ‘Kano To Califonia’. Haka kuma ya shahara a soshiyal midiya, inda ya ke amfani da wata sara da ya ke cewa, “Me Ya Faru?” Mutane da dama sun ɗauki wannan sarar tasa.
Allah ya ba su zaman lafiya da zuria’a ɗayyiba, amin.

