• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, July 15, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Jaruman Kannywood, Abdul M. Shareef da Maryam Malika sun zama ɗaya

by Editors
June 27, 2025
in Uncategorized
0
Jaruman Kannywood, Abdul M. Shareef da Maryam Malika sun zama ɗaya

Amarya Malika da ango Abdul M. Shareef a wurin dinar auren su

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

BURIN jaruman Kannywood, Abdul’azeez Muhammad Shareef (Abdul M. Shareef) da Maryam Muhammad Ƙaura (Maryam Malika) ya cika a yau domin kuwa an ɗaura masu aure.

An ɗaura auren Abdul da tsaleliyar sahibar tasa a yau Juma’a da misalin ƙarfe 1:15 na rana, bayan an gama sallar Juma’a a Masallacin Sani Zangon Daura da ke Unguwar Kaji, Kaduna, a bisa sadaki N200,000.

Ango Abdul M. Shareef tare da masoya a wurin ɗaurin auren sa a yau
Daga hagu: Musa Mohammed Abdullahi, Ali Nuhu, da Tijjani Faraga a wurin ɗaurin auren

Wasu daga cikin ‘yan fim ɗin da suka halarci ɗaurin auren sun haɗa da Shugaban Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya (NFC), Alhaji Ali Nuhu, da Malam Tijjani Faraga, Malam Musa Muhammad Abdullahi, Sanusi Oscar 442, Daddy Hikima, Mustapha Nabraska, Naziru Ɗanhajiya, Nasiru Naba, Nura MC Khan, Umar Gombe, Lawal Ahmad, Waziri Garba Bado, Hannafi Rabilu Musa, Hamza Talle Maifata, Salisu S. Fulani da ƙanen ango, wato Umar M. Shareef.

Kafin ranar ɗaurin auren, an yi shagulgula da suka haɗa da wankan amarya (bridal shower), ƙwallon ƙafa da dina.

A ranar Talata da ta gabata ne aka gudanar da wankan amarya ɗin a ɗakin taro na otal ɗin Hamdala da ke Titin Muhammadu Buhari. Sai dai bikin na mata ne zalla.

A shekaranjiya aka buga wasan ƙwallon ƙafa na sada zumunci tsakanin abokai (friendly match), a filin wasa na otal ɗin Hamdala. ‘Yan fim da dama, musamman na Kaduna, sun halarta.

Sai kuma jiya aka gudanar da ƙasaitacciyar dina, inda ‘yan Kannywood maza da mata daga jihohin Kano, Katsina, Jos da Kaduna suka haɗu.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa Abdul yana da mata ɗaya da ‘ya’ya biyar, ita kuma Maryam tana da ‘ya’ya uku a gidan tsohon mijin ta.

Ango yana gaisawa da abokan arziki a wurin ɗaurin auren

Loading

Previous Post

Gwamnatin Tarayya ta bada tabbacin akwai tsaro a Abuja duk da gargaɗin da Amurka ta ba matafiya

Next Post

MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 

Related Posts

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano
Labarai

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano

July 11, 2025
Nijeriya

Tinubu yana goyon bayan Ƙananan Hukumomi su ci gashin kan su – Minista

July 11, 2025
Nijeriya

Shirin Sabunta Fata na Tinubu yana samar da damarmakin cigaba — Minista

July 10, 2025
Ranar Murna

Furodusa a Kannywood, Rabi’u Koli zai yi aure ranar Asabar

July 10, 2025
Labarai

Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 

July 10, 2025
Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista
Nijeriya

Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista

July 10, 2025
Next Post
MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 

MOPPAN ta yi wa al'ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!