JARUMA, babbar furodusa a Kannywood kuma ‘yar siyasa a Kano, Rashida Adamu Abdullahi (Maisa’a), ta yi nuni da cewa idan har gwamnatin Kano ba ta soke dokar hana baburan A Daidaita Sahu bin wasu tituna a Kano ba, to da wuta jam’iyyar APC ta ci zaɓe a jihar da ma Nijeriya ba ki ɗaya.
Jarumar bayyana takaicin ta dangane da dokar ta gwamnatin wadda ta fara aiki ne daga yau Laraba, 30 ga Nuwamba, 2022.
Rashida dai ƙusa ce a tafiyar gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje, inda har an ba ta muƙamin mai ba gwamna shawara.
Jarumar ta saki wani guntayen bidiyo guda uku a soshiyal midiya, musamman TikTok da Instagram, inda ta bayyana alhinin ta kan sabuwar dokar.
A bidiyon farko, wanda a kan sa ta rubuta, “Wannan wace irin masifa ce,” furodusar ta ce: “In dai ana so APC ta ci zaɓe a Jahar Kano, wallahi maganar A Daidaita Sahu a janye ta.
“An ce ‘yan A Daidaita Sahu su rinƙa tashi daga ƙarfe goma. Baba, sun ɗauki wannan maganar da aka gaya masu.

“Zaɓe ya ƙarato, idan mu ka rasa ‘yan A Daidaita Sahu a Kano wallahi mun shiga uku. A taimaka wa Dakta Nasiru Yusuf Gawuna. In dai ana son ya ci gwamnan nan a Jahar Kano, da shi da Murtala Sulen Garo, a janye maganar A Daidaita Sahu don girman zatin Allah, Baba Ganduje.
“Ba mu ɗauko hanyar cin zaɓe ba! Ba mu ɗauko hanyar cin zaɓe ba! Duk wanda ya faɗi wannan maganar ‘yan A Daidaita Sahu, wallahi ba ya so mu ci zaɓe a Jihar Kano.”
A bidiyo na biyu da ta yi, Rashida ta bayyana cewa su magoya bayan APC su na faɗi-tashi a kullum don ganin an samu nasara, amma sai gwamnati ta riƙa zuwa ta na aikata abin da bai dace ba.
Ta ce to ita dai ba za ta yi shiru ba a game da wannan dokar, ya zama dole ta yi magana ko da kuwa a za tsire ta.
A bidiyo na uku, wanda akwai alamar ya na da alaƙa da sauran biyun, an ga jarumar ta na tafiya a mota ta na jin waƙar Ali Jita inda ya ke faɗin: “Allah sarki duniya, idan wani ya ƙi ka wani ya bar ka, wani zai so ka!”