ALLAH ya azurta jarumi a Kannywood, Adam M. Adam, da ƙaruwar ‘ya mace a ranar Laraba da ta gabata.
Maiɗakin sa ta haifi jaririyar a Kano, kuma an raɗa mata suna Fatima.
Adam M. Adam wanda ake kira Mai Gaskiya, ya shaida wa mujallar Fim irin fatan cikin sa dangane da haihuwar, inda ya ce: “Fatima ita ce ‘ya ta ta uku da Allah ya ba ni, don haka ina godiya ga Allah da ya sa aka haife ta lafiya kuma a cikin wannan wata mai alfarma na Ramadan. Alhamdu lillah, ina ƙara yi wa Allah godiya.”