JARUMI a Kannywood, Shariff Aminu Ahlan, ya bayyana irin kewar mahaifiyar sa da ya ke yi tun bayan rasuwar ta shekara tara da ta gabata.
A yau Lahadi, 1 ga Janairu, 2023 mahaifiyar tasa ta cika shekara tara cif da rasuwa.
Ahlan ya yi rubutu a Instagram, ya ce, “Shekara tara, ‘nine years’ kenan. Kamar yanzu ne Hajiya ta. Na yi rashin uwa. ‘The best mother in the world’.”
Ya cigaba da cewa: “Kin so ni Hajiya, kin ban daɗi, kin nunan hanyar da ake nema ake samun abin jin daɗin, kin ban ilimi wanda yanzu shi ne gata na da rufin asiri, kin yi haƙuri da ni Hajiya ta, kin sha fama san da kai na na rawa, kin min addu’a ba dare, ba rana, har a san da Allah ya kira ki ki na zaune da carbi bayan sallar asuba.
“Ba don ke ba Hajiya ta da Allah kaɗai ya san yau a wane yanayi zan kasance, in ma na san a ina na ke. Addu’ar ki ce ta yi tasiri, kuma ita ta ke bi na, da yanzu na tsinci kai na cikin rufin asiri da wadata.
“Allah ya jiƙan ki, Hajiya ta. Ina ma a ce har yanzu ki na nan ki ga abin da ki ka riƙa faɗa ya na tabbata. Alhamdu lillah, Alhamdu lillah, Alhamdu lillah!
“Allah ya sada ki da wanda ki ka fi so Muhammad, (SAW).”
Jarumin ya wallafa tsokacin tare da hoton da ya ɗauka shi da gyatumar tasa.
Wannan rubutu da Ahlan ya janyo masa tausayawa daga ɗimbin mabiyan sa a soshiyal midiya, inda su ka riƙa yi wa Hajiyar tasa addu’ar neman rahamar Allah.