JARUMI kuma furodusa a Kannywood, Malam Aminu Shehu (Mirror) zai ƙara aure a gobe Asabar.
Malam Aminu, wanda shi ne mamallakin kamfanin Mirror of the Moment da ke Zariya, Jihar Kaduna, a yanzu an fi sanin sa da sunan Malam Zaidu a cikin shirin ‘Gidan Badamasi’ da ake nunawa a tashar Arewa 24.
Za a ɗaura auren sa da sahibar sa A’isha Ɗalhatu (Baby) ne a gobe da misalin ƙarfe 2:30 na rana, a gida mai lamba 2, gidan Manu da ke Unguwar Makama Dodo, Ƙofar Galadima a cikin birnin Zariya.
Katin gayyatar ya nuna za a haɗu a gida mai lamba, 261, gidan Wanzamai, Kusfa, Zariya.
Jarumin ya buƙaci duk wanda bai samu damar halartar ɗaurin auren ba da ya yi masu addu’a.