SHAHARARREN jarumi kuma mawaƙi a Kannywood, Yakubu Mohammed, ya ɗauki nauyin karatun wasu yara biyu daga Ƙaramar Hukumar Wudil da ke Jihar Kano waɗanda aka nuno suna rera yaren Aluta.
Yakubu ya ɗauki nauyin karatun Bashir Yahaya Ubale da Muhammad Inuwa tun daga firamare har zuwa jami’a.
Maƙasudin ɗaukar nauyin karatun yaran, shi ne sakamakon wani bidiyo da wani ɗalibin Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kano (KUST) da ke Wudil, mai suna Muhammad Sudais, ya wallafa a Facebook yaran su na Aluta irin wanda ɗaliban jami’a ‘yan gwagwarmaya su ke yi a harabar jami’ar.
Wannan ya ba Yakubu sha’awa, shi ma sai ya ɗauka ya ɗora a Facebook da Instagram.
Daga baya, sai ya nemi a nemo masa inda yaran suke, sai shi Muhammad Sudais da wata Ummukhursum su ka nemo masa bayanan inda yaran su ke.
Yakubu ya ziyarci yaran da iyayen su, inda ya gana da su.
Sannan ya sa Ummukhursum ta nemo masa makarantar kuɗi da ya kamata a saka su.
Ummukhursum ta nemo wata makaranta mai suna De Fountain Knowledge Academy, a Wudil, aka yi wa Bashir da Muhammad rajista, ta yadda da zarar an koma makaranta a Satumba za su fara zuwa makaranta.
A yayin ziyarar, Yakubu ya saya wa yaran kayan sawa, kuma a lokacin su ka canza kaya, sannan ya ɗebe su zuwa makarantar da aka yi masu rajista.
Bashir da Muhammad tare da iyayen su sun yi matuƙar farin ciki da wannan cigaba da su ka samu.
Haka kuma sun yi wa Yakubu addu’o’i da godiya.

Aluta dai kalma ce da aka fi amfani da ita a cikin ƙasashen Afrika don yin nuni ga gwagwarmaya ko yaƙi da zalunci, rashin adalci na zamantakewa, ko ko wani nau’i na zalunci ko cin hanci da rashawa. Ya ƙunshi ra’ayin haɗin kai da tsayin daka don samun ‘yanci da daidaito.
Ana danganta kalmar sau da yawa tare da ƙungiyoyin ɗalibai, ƙungiyoyin ƙwadago, da gwagwarmayar siyasa.
Aluta ta ƙunshi ƙudirin ƙalubalantar tsarin mulki da bayar da shawarar kawo sauyi ta hanyar zanga-zangar da aka shirya da sauran nau’o’in tsayin daka.