TO, shi ma dai makaɗi, mawaƙi kuma jarumi a Kannywood, wato Kabiru A. Zango KB Zango, ƙane ga jarumi Adam A. Zango, ya yi bankwana da kwana a situdiyo.
Yau Juma’a, 26 ga Mayu, 2023 aka ɗaura auren sa da masoyiyar sa Haleema Bello Abdullahi (Umaima).
An ɗaura auren da misalin ƙarfe 2:30 a Masallacin Juma’a na Tudun Wada, Gombe, a kan sadaki N100,000.

Wasu daga cikin waɗanda su ka halarci ɗaurin auren sun haɗa da Usman Mu’azu, Nasiru Naba, Saifullahi Safzor, Ibrahim Saminaka, Rabi’u A. Zango da Sa’ad Sani (Cousin).
Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba.

Allah ya basu zaman lafiya