A RANAR Litinin mai zuwa, 30 ga Disamba, 2019 za a yi babban taro na gabatar da wani littafin koyon Turanci wanda fitaccen furodusa kuma malamin Turanci Kabiru Musa Jammaje ya rubuta.
Sunan littafin mai suna “The 1000 Words, Via Freedom Radio”.
Za a gudanar da taron ne a babban zauren Gidan Mambayya da ke unguwar Gwammaja a cikin garin Kano.
A taron, za a baje kolin waƙoƙi na fasaha da kuma jawabai daga masana a kan harshen Turanci.
Babban baƙo mai jawabi shi ne tsohon Babban Sakataren Hukumar Jami’o’i ta Ƙasa (NUC), Farfesa Munzali Jibrin na Jami’ar Bayero, Kano.
Mujallar Fim ta nemi jin ta bakin Jammaje dangane da wannan taron, inda ya ce, “Shi wannan taro an shirya shi ne domin gabatar da littafin ‘The 1000 Words, Via Freedom Radio’ wanda kalmomi ne guda dubu na haɗa su wanda na ke gabatarwa a cikin shirin da na ke yi na koyar da Turanci.
“Duk da cewar tsawon shekara 13 ina gabatar da shirin, amma su waɗannan kalmomi na shirin da na gabatar ne a cikin shekaru uku, na haɗa su na mayar da su littafi, domin tsawon lokacin da na yi ina gabatar da shirin mutane su na ta tambaya ko littafi ne, sai na ba su amsa da cewar ba littafi ba ne, bincike ne na yi a cikin kalmomin Turanci na samo su. To sai na ga akwai buƙatar na haɗa su su zama littafi domin samar wa matasa hanyar ƙaruwar ilimi.
“To wannan ta sa aka samar da littafin kuma a yanzu ake shirin gabatar da shi domin amfanin jama’a.”
Dangane da burin da ake so a cimma wajen gabatar da littafin kuwa, cewa ya yi, “To, gani mu ka yi bai kamata mu saki littafin haka lami ba, don haka mu ka ga akwai buƙatar a ɗan yi laccoci a yi taro, domin a zaburarar da mutane, kuma a ƙara musu ilimi a kan abin da ya shafi yaren Turancin, da kuma al’adu. Don haka ne mu ka shirya taron, don ya zama ba kawai littafi aka saka ba, har ma a ƙaru da abin da manyan malamai za su faɗa.
“Sai dai kuma mutane su sani, wannan abu ne sabo, domin a gidan rediyo ake jin shirin, sai kuma aka buɗa abin ya zama littafi, kuma aka ƙara buɗa abin ya zama taro na bada lacca da kuma waƙoƙi.
“Kuma wani ƙarin abin sha’awa ma, duk wata kalma da ake ganin faɗar ta da Turanci ta na bada wuya, mun mayar da ita da kalmar Hausa domin sauƙaƙa wa masu koyo domin amfanin yau da kullum, baya ga amfani da mu ka yi da sassauƙan Turanci.
“Don haka wannan taro ne na kowa da kowa.
“Sai dai kuma akwai wani tsari da aka yi ga masu buƙatar shiga domin kada ya zama taron inna-rududu, yadda zai zama mun kasa samun wajen da za mu ajiye mutane, don haka ne mu ka kawo ƙa’ida ta yin rajista: mutum ya je ya yi rajista ya shiga. Kuma ba wani kuɗi mai yawa mu ka sa ba, kuma akwai abubuwa da za ka samu a cikin taron idan ka yi rajista har ma da kwafin littafin, don haka abin zai zama riba ne ma a gare ka.”
Daga ƙarshe, malamin ya yi kira ga waɗanda za su shiga taron da cewa su fahimci taron manufar sa ita ce ƙarfafa wa matasa domin su tashi su nemi ilimi domin cigaban rayuwar su.