MUJALLAR Fim ta samo bidiyon hirar da aka yi da daraktan fim ɗin ‘Mai Martaba’, wato Prince Daniel (Aboki) inda yake faɗin an nuna masa ƙi a Kannywood saboda shi ba Musulmi ba ne a lokacin da ya zo.
A yau ne daraktan mai tashe ya yi kakkausan martani ga labarin da jaridu suka buga, ciki har da mujallar Fim, inda ya ƙaryata zancen cewa an ƙi yarda da shi a Kannywood a farkon zuwan sa.
Labarin da aka buga an gina shi ne kan tattaunawar da wani bature ya yi da Prince Daniel (Aboki) a kan dandamali a zauren bikin baje-kolin finafinai na shekara-shekara na Nollywood in Hollywood wanda aka yi a farkon wannan watan a birnin Los Anjalis na ƙasar Amurka.
Daraktan da wanda yake hira da shi suna zaune a gaban jama’a ‘yan kallo, suna tattaunawa kan nasarori da wahalhalun da su Aboki suka ci karo da su wajen shirya fim ɗin nasa.
A daidai wata gaɓa, sai mai yi masa tambayoyin ya ce masa wannan fim dai ya bambanta da irin waɗanda ake shiryawa a kudancin Nijeriya, to yana so ya san irin ƙalubalen aka ci karo da su wajen shirya fim musamman a arewacin Nijeriya.
Nan take sai Aboki ya amsa da cewa:
“Yes so, a lot of it. I mentioned somewhere that as a filmmaker I got trapped during this production, trapped because I’m from the North, northern part of Nigeria, but I am Christian, and the Kannywood is a predominantly Muslim industry. And the Nollywood part of the industry is predominantly Christian. So, I became trapped because at some point the Kannywood didn’t quite accept me because of religion, and Nollywood didn’t accept me because of region.
So, this side see me as a Christian practising — from the Kannywood side of the industry — and then the other side see me as a Northerner practising in Nollywood.
“So, but the dynamics changed when the film eventually got selected to represent Nigeria at this year’s Oscars. Everything changed.”
Wannan ba sai an fassara ba, domin fassarar tana cikin labarin da aka buga da farko, wanda darakta Aboki ya ce ba haka ya faɗa ba.
Kalli bidiyon a nan: