A JIYA Juma’a, 23 ga Disamba, 2022 aka ɗaura auren mawaƙin siyasa a Kannywood, Ibrahim Shehu Suleiman, wanda aka fi sani SS Danko.
An ɗaura auren sa da amaryar sa, Nusaiba Shu’aibu, da misalin ƙarfe 2:30 na rana, a Ƙofar Gayan, daura da Kogoro, Zone II, lamba 17, Abbas Street, Zariya, Jihar Kaduna, a kan sadaki N100,000.
Bayan ɗaurin auren an yi walima a wani gidan cin abinci da ke cikin garin Zariya.

Wasu daga cikin waɗanda su ka halarci ɗaurin auren sun haɗa da Sagir Baban Kausar, El-Mu’az Birniwa, Ashiru Ɗan Auta, Auta Waziri, Iƙira Shuwares, Malan Waƙa, Ashraf Kano, Auta MG Boy, Abdul Kafinol, Iliya Zariya, Salisu Silinda, M. Suraj, Daddy R & B da IBB Brnin Yawuri.
Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba, amin.
