MASANA’ANTAR finafinan Indiya ta girgiza sakamakon rashin da ta yi na manyan jarumai biyu a tsakanin jiya da yau, wato Irfan Khan da Rishi Kapoor.
Dukkan su sun rasu ne sakamakon ciwon daji, wato kansa. Irrfan ya rasu jiya, sannan Kapoor ya rasu a yau.
Kowannen su ya mutu ne a asibiti, duk a babban birnin ƙasar, wato Mumbai, kuma ɗaya Musulmi ɗaya mabiyin addinin Hindu.
Sahabzade Irfan Ali Khan, wanda aka fi da suna Irrfan Khan, an haife shi ne a ranar 7 ga Janairu, 1967.
Ya shafe sama da shekara 30 ya na fitowa a fim. Ban da finafinan Indiya, ya fito a wasu finafinan Birtaniya da na Amurka.
Ya ci kyaututtuka da su ka haɗa da ‘National Film Award’, ‘Asian Film Award’, da kuma ‘Filmfare Awards’ guda huɗu. A cikin 2011 aka ba shi kyautar Padma Shri, wadda ita ce kyautar karramawa ta huɗu mafi girma a ƙasar Indiya.
Shi dai Irrfan Khan, ya fara fitowa ne a fim ɗin ‘Salaam Bombay!’ a 1988, inda aka ba shi ƙaramin rol bayan ya sha fama a rayuwa.
Fitowar da ya yi a wani fim ɗin Birtaniya mai suna ‘The Warrior’ a 2001, ita ce ta buɗe masa ƙofa har aka sa shi a fim ɗin ‘Haasil’ (2003) da ‘Maqbool’ (2004).
Daga nan ya fito a babban rol a cikin ‘The Namesake’ (2006), ‘Life in a… Metro’ (2007), da kuma ‘Paan Singh Tomar’ (2011) inda a matsayin sa na jarumin shirin aka ba shi kyautar ‘National Film Award for Best Actor’.
Ƙofa ta buɗe masa, ya ci gaba da fitowa a manyan finafinai da su ka haɗa da ‘The Lunchbox’ (2013), ‘Piku’ (2015), ‘Talvar’ (2015) da finafinan Amurka ɗin nan ‘The Amazing Spider-Man’ (2012), ‘Life of Pi’ (2012), ‘Jurassic World’ (2015), da ‘Inferno’ (2016).
Haka kuma ya ciri tuta a finafinai da su ka haɗa da ‘Slumdog Millionaire’ (2008), ‘New York’ (2009), ‘Haider’ (2014), da ‘Gunday’ (2014).
Fim ɗin sa na Indiya wanda ya fi wazgo riba shi ne wani na ban-dariya mai suna ‘Hindi Medium’ (2017), wanda har ya sa aka karrama shi da kyautar ‘Filmfare Award for Best Actor’.
Fim ɗin ƙarshe na Irrfan shi ne cigaban shirin ‘Hindi Medium’ wanda aka sa wa suna ‘Angrezi Medium’ na darakta Homi Adajania, wanda aka saki a ranar 13 ga Maris, 2020.
An ce ya zuwa shekara ta 2017, finafinan sa sun samu cinikin dalar Amurka har biliyan 3.6.
Tun a watan Maris, 2018, Khan ya tura saƙo a Twitter inda ya bayyana cewa an auna shi an gano cewa ciwon kansa (‘neuroendocrine tumor’) ya kama shi. Sai ya tafi neman magani a Ingila inda ya shekara ɗaya, ya koma gida a cikin Fabrairu 2019.
An kwantar da shi a asibitin ‘Kokilaben Dhirubhai Ambani Hospital’ da ke Mumbai a shekaranjiya, 28 ga Afrilu, 2020, inda aka fara yi masa magani. Sai dai kash! gari na wayewa ya ce ga garin ku.
Ya mutu ya bar matar sa, marubuciya Sutapa Sikdar, da ‘ya’yan su maza guda biyu.
Manyan ‘yan fim na Bollywood da dama sun tura saƙon ta’aziyyar rasuwar Irrfan Khan, cikin su har da Amitabh Bachchan da Kamal Hassan.
Ana cikin jimamin wannan rasuwar kuma sai aka wayi gari yau da labarin rasuwar shahararren jarumi Rishi Kapoor.
Shi kuma ya mutu ne ya na da shekara 67 a duniya domin kuwa an haife shi ne a ranar 4 ga Satumba, 1952.
Ya fara fitowa a fim tun ya na ƙaramin yaro, inda ya taka rol a fim ɗin mahaifin sa Raj Kapoor mai suna ‘Mera Naam Joker’, wanda aka saki a cikin 1970. Sakamakon rol ɗin ya sa aka ba shi kyautar ‘National Film Award for Best Child Artist’.
Fim ɗin sa na farko a matsayin jarumin shirin shi ne fitaccen fim ɗin nan na soyayya, wato ‘Bobby’ (1973), inda ya fito tare da jaruma Dimple Kapadia. Rol ɗin sa ya sa aka karrama shi da kyautar ‘Filmfare Award for Best Actor’.
Kapoor ya fito a matsayin jarumin finafinan soyayya har guda 92 a tsakanin 1973 zuwa 2000.
Wasu daga cikin manyan finafinan sa su ne ‘Khel Khel Mein’ (1975), ‘Kabhi Kabhie’ (1976), ‘Amar Akbar Anthony’ (1977), ‘Karz’ (1980) an??da ‘Chandni’ (1989.
Daga shekarar 2000, ya riƙa fitowa a fim a matsayin wani mutum da aka sani a zahiri. Irin waɗannan finafinan sun haɗa da ‘Love Aaj Kal’ (2009), ‘Agneepath’ (2012), da ‘Mulk’ (2018).
An karrama shi da kyautar ‘Filmfare Critics Award for Best Actor’ saboda rol ɗin da ya taka a cikin ‘Do Dooni Chaar’ (2010), sannan aka ba shi kyautar Filmfare Award for Best Supporting Actor’ saboda rol ɗin sa a fim ɗin ‘Kapoor & Sons (2016).
Bugu da ƙari, an karrama shi da
kyauta mafi daraja a Bollywood, wato ‘Filmfare Lifetime Achievement Award’, a cikin 2008.
Fim na ƙarshe da ya fito a ciki shi ne ‘The Body’ (2019).
Sau da yawa, Rishi Kapoor ya kan fito a fim tare da matar sa, fitacciyar jaruma Neetu Singh, wadda su na da ‘ya’ya biyu da ita, ciki har da jarumin nan Ranbir Kapoor.
Tun a cikin 2018 aka auna Kapoor aka gano cewa cutar kansa ta kama shi. Sai ya tafi neman magani a birnin New York na ƙasar Amurka inda ya yi jinya har zuwa watan Satumba da ya gabata, lokacin da ya koma gida.
A jiya ne aka garzaya da shi asibiti mai suna ‘Sir HN Reliance Foundation Hospital’ da ke birnin Mumbai bayan ya yi kukan cewa numfashin sa ya na ɗaɗɗaukewa.
A daren jiya ya yi ta wasa da dariya da likitoci da sauran ma’aikatan asibitin.
A wata sanarwa da iyalan sa su ka bayar a yau, sun ce Rishi Kapoor bai damu da komai ba a wannan lokaci, illa iyaka batun iyali, abokai, abinci da finafinai.
A yau da safe shi ma ya ce ga garin ku. Ba tare da ɓata lokaci ba aka kai shi wani waje inda aka ƙone gawar sa, ta koma toka, kamar yadda addinin su na Hindu ya tanada.
A sanarwar da iyalan sa su ka bayar, sun ce: “Ya gode da soyayyar da masoyan sa su ka nuna masa daga ko’ina a faɗin duniya. A mutuwar sa, duk za su fahimci cewa shi ya fi so a riƙa tuno da shi tare da murmushi, ba da zub da hawaye ba.”
Shi dai Rishi Kapoor, ya fito ne daga gidan hamshaƙan masu shirya finafinan Indiya, wato gidan Kapoor, waɗanda sun daɗe da mamaye harkar fim a ƙasar.
Rishi Kapoor dai kawu ne ga fitattun jaruman nan mata, wato Karisma Kapoor da Kareena Kapoor-Khan.
‘Yan fim da ‘yan siyasa na Indiya sun yi caa wajen bayyana alhinin su game da mutuwar sa.
Amitabh Bachchan ya ce wannan mutuwa ta ragargaza shi, yayin da Firayim Minista Narendra Modi ya ce Rishi Kapoor “babbar ma’adanar fasaha ce,” ya ƙara da cewa zai cigaba da tuno irin mu’amalar da su ka yi, har ma a soshiyal midiya.
Shi kuma Shugaban Ƙasar Indiya, Sri M. Venkaiah Naidu, cewa ya yi ya shiga “zurfin baƙin ciki” da ya samu labarin mutuwar Rishi Kapoor.