MAI Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yi kira ga masu gudanar da harkar fim na masana’antar Kannywood da ma na Afirka baki ɗaya da su riƙa kiyayewa wajen aikin su a game da cusa al’adu marasa kyau da za su kawo lalacewar tarbiyyar yara masu tasowa nan gaba.
Sarkin ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke gabatar da jawabi a wajen taron buɗe Bikin Baje-kolin Finafinan Harsunan Afirka na Kano, wato ‘Kano Indigenous Languages of Africa Film Market and Festival’ (KILAF), kashi na 5, wanda aka gudanar a daren Talata, 22 ga Nuwamba, 2022 a Gidan Ɗanhausa da ke unguwar Nassarawa G.R.A. a Kano.
Alhaji Aminu, wanda Turakin Kano, Alhaji Abdullahi Lamiɗo Sunusi Bayero, ya wakilta a taron, ya ƙara da cewa: “Mu a wannan nahiya mu na da al’adu masu kyau da duk duniya ake alfahari da su, amma a wajen gudanar da finafinan mu sai mu ka fi karkata ga ɗauko wasu baƙin al’adun da su ke zama koma-baya a cikin mu.

“Don haka wannan biki da ake shiryawa na Baje-kolin Finafinan Afirka, ya kamata ya zama masu gudanar da harkar fim sun samar da tsarin yin amfani da al’adu da kuma koyi da kyawawan ɗabi’u da mu ke da su, wanda kuma shi ne manufar shirya taron.”
Tun da farko da ya ke jawabin maraba, jagoran shirya taron, Malam Abdulkareem Muhammad, ya yi wa Allah godiya da ya kawo wannan lokacin na shirya taron karo na 5 wanda kuma, a cewar sa, abin alfahari ne.
Malam Abdulkareem ya miƙa godiya ta musamman ga baƙin da su ka zo bikin daga ƙasashe daban-daban kamar Afirka ta Kudu, Kenya, Ingila, Nijar da Faransa.
Ya ce: “Haka nan su ma baƙin mu na gida da su ka zo daga jihohi daban-daban mu na yi masu maraba. Mu na fatan za a yi wannan taron har zuwa ƙarshen sa cikin nasara.”
Shi ma wakilin Ministan Al’adu na Jamhuriyar Nijar, Malam Lawwali Boka, a nasa jawabin, ya bayyana Nijar da Nijeriya a matsayin ƙasashen da su ke a matsayin ƙasa ɗaya ta fuskar addini da kuma al’adu, don haka babu wani abu da ya bambanta harkar fim a Nijar da kuma Nijeriya, saboda haka za su haɗa kai domin samar da finafinai masu raya al’adun gargajiya da kuma cusa ɗabi’u masu kyau a cikin matasa.

An dai yi jawabai da dama a wajen, kuma daga ƙarshe aka kammala da dina.
Masu rawar ƙoroso kuma sun nishaɗantar da mahalarta.
Cikin fitattun jaruman Kannywood da su ka halarci wajen akwai Ali Nuhu, Abba Al-Mustapha T.Y. Shaban, da Baballe Hayatu.

