A RANA ta biyar ta taron KILAF Awards 24 da ake yi yanzu, an shirya wa mahalartan da suka zo daga ciki da wajen ƙasar nan yawon buɗe ido na nuna muhimman wuraren tarihi a cikin garin Kano.
Farko an kai baƙin Gidan Ɗanhausa da ke Titin Sokoto a Unguwar Nassarawa GRA, da kuma ɗayan da ke kusa da Ma’aikatar Ayyuka duk dai a cikin Unguwar Nassarawa ɗin, domin su ga kayan tarihi.
Haka nan an kai su Gidan Makama wanda shi ma gidan adana kayan tarihi ne na ƙasar Hausa da ke kusa da Ƙofar Kudu.
Sai kuma gidan Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ll da shi ma wani ɓangare ne na abubuwan tarihi a birnin Kano.
An kammala zagayen da zuwa Dutsen Dala da Gwauron Dutse baƙin suka hau suka ga abubuwan tarihi da na al’adun Kano da ƙasar Hausa.
Da ƙarfe 4 na yamma aka dawo muhallin taron da ke Jami’ar Bayero inda aka ci gaba da nuna finafinan Afrika da suke nuna yare da kuma al’adun nahiyar, har zuwa ƙarfe 6.
Da ƙarfe 8 na dare aka shirya liyafar fitar da sunayen waɗanda suka shiga gasa a matakin na biyun ƙarshe.
An shirya taron a otal ɗin Tahir Guest Palace da ke cikin Nassarawa GRA kuma an samu muhimman mutane da suka halarta.