* An rantsar da sabbin shugabannin ANA Kano
* Zan ɗora a inda tsohon shugaba ya aje, inji Tijjani Muhammad Musa
SHAHARARREN shaihun malamin adabi kuma marubuci, Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo, ya yi kira ga sababbin shugabannin Ƙungiyar Marubuta Nijeriya ta Nijeriya (Association of Nigerian Authors, ANA), reshen Jihar Kano, da su maida hankali wajen tsare gaskiya da yin adalci tsakanin mambobin ƙungiyar da su ke jagoranta.
Farfesan ya yi kiran ne a wajen taron rantsar da shugabannin ƙungiyar wanda aka yi jiya Lahadi, 4 ga Yuli, 2021 a babban ɗakin taro na Laburaren Murtala Muhammed da ke Kano.
Wakilin mujallar Fim, wanda ya halarci taron, ya ruwaito cewa Ɗangambo ɗin ne ya rantsar da sababbin shugabannin, inda jim kaɗan bayan rantsarwar ya gabatar da jawabi, ya na faɗin, “Komai za ka gina, ka gina shi kan gaskiya, ya zama cewa wannan abu da za ka yi ya zamto cewa wannan abu da zan yi ya zamto kan doron gaskiya ko kuwa ya saɓa?
“Doron gaskiya ya haɗa da addinin mu na Musulunci, ya haɗa kuma da al’adun mu na Hausawa, ba al’adun Turawa ba, da kuma abin da ya ke bai saɓa wa rubutu ba.”
Ɗangambo ya ce masu, “Kun sani cewa ita wannan ƙungiya, ƙungiya ce ta marubutan Nijeriya baki ɗaya. Ina ganin a sauran fannoni ban da Hausa, wadda ni zan ce shi na sa gaba kuma ita na ke ganin ta haɓaka, to kuma ya na cikin naku.
“Amma sauran harasa su ma sai mu ce kar a bar su a baya. Ku yi duk abin da za ku yi don ganin an gudanar da cigaban wannan ƙungiya. Ku farfaɗo da ita sosai kuma ku ba su muhimmanci.”

Farfesan ya bayyana ANA a matsayin ta kowa da kowa, ba wai iya Musulmi ba. Ya ce, “Ku jawo kowa da kowa domin ya bada gudunmawa. Ba wai an ce wannan ƙungiya ta iya Musulmi ba ce tunda ƙungiya ce ta marubutan Nijeriya, don haka ko ma ba Musulmi ba ne in dai ka na rubutu za ka iya shigowa ka bada gudunmawar da mutum ya ga zai iya.”
Shaihin malamin, wanda ya shahara ne wajen aikin koyarwa da ya yi har ya kai ga ritaya a Jami’ar Bayero, Kano, ya kuma shawarci zaɓaɓɓun shugabannin na ANA da su kwana da sanin cewa amana ce Allah ya ɗora masu su tafiyar da ita ta hanyar kwatanta adalci ga kowa.
Ya yi addu’ar Allah ya ba su ikon sauke nauyin da aka ɗora musu.
A nasa jawabin, sabon shugaban ƙungiyar, Malam Tijjani Muhammad Musa, ya yi godiya ga Allah bisa wannan jagoranci da Allah ya ba shi tare da bayyana ƙudirin cigaba da ayyuka na cigaban ƙungiyar, haɗi da samar da haɗin kai tsakanin ‘ya’yan ta kamar yadda shugaban da ya gada ya faro.
Tijjani ya ce, “Ƙungiya ce wacce da farko ta samu tangarɗa, amma Allah cikin ikon shi tunda daga shugaban da ya sauka wanda na yi wa sakatare ya karɓi wannan ragamar tafiyar, duba da yadda wasu su ka ɓalle sakamakon an ɓata musu rai a wannan tafiya, su ka yi zuciya, amma haka mu ka dinga bin su mu na dawo da su domin ganin an dawo da martabar wannan ƙungiya, Allah cikin ikon sa daga shekara biyu da mu ka yi ni da tsohon shugaba wanda kuma mu ka ƙara dawowa mu ka yi wasu biyun, wanda daga shi ne na hau yanzu, mun yi ƙoƙari wajen ganin abubuwa sun saisaita.”
Har ila yau, malamin ya yi duba da yadda aka samu wancan cigaba a lokacin da ya ke matsayin sakatare, ya ce hakan ta sa yanzu ya yi wa tafiyar tasa ta ke da ‘Ɗori a kan Ayyukan Baya’.
Tijjani ya ce, “A haƙiƙanin gaskiya, idan mu ka ɗora daga inda tsohon shugaba ya tsaya to dai lashakka ANA za ta zama abin da mu ke ta buri ta zama.
“Mu na nan mun yi shirye-shirye daban-daban, domin kuwa wanda wasu ma dai sai dai mu yi iya yin mu a matsayin mu na shugaba har zuwa lokacin mu ya ƙare mu sauka mu bar wa wasu su ɗora a kai. Ba wai wasu su zo su kawo manufofin su na daban ba, wasu ma su zo su yi nasu daban ba, ya zo kuma ba su ƙarasa ba lokacin su ya yi ba, su yi komai ba shi ya sa in dai an ɗauki wannan tsarin a haka abubuwan za su taɓarɓare mana, su na lalace mana. Amma tsarin da mu ka yi na abubuwan da tsohon shugaba ya ɗora a kai ya yi, to shi mu ma za mu ɗora a kai.
“Akwai abubuwa da yawa da ya ɗauko amma bai kai ga ya cimma burin sa ba saboda rashin lokaci. To za mu ɗora a kai in Allah ya yarda.”

Shugaban ya ƙara da cewa abubuwan da za su ɗora a kai sun haɗa da:
1. Shigo da kafafen sadarwa domin sanar da mutane irin halin da ƙungiyar ANA ta ke ciki.
2. Shigo da marubuta cikin ƙungiya waɗanda su ke da baiwar rubutu amma jin kunya da jin nauyi ya sanya sun kasa bayyana baiwar su ko kuma rashin sanin ya za su iya, rubutun nasu ya dakushe ba don komai ba sai don ganin cewa a kulli yaumin idan mutum ya yi rubutu ya san cewa manufar al’ummar mu ake yaɗawa.
Ya ce, “Mutane ne su ke zuwa daga wasu ƙasashen su na rubutu a kan Hausawa, su faɗi duk abin da su ke so tsaf dangane da abincin mu, suturar mu, al’adun mu da ire-iren waɗannan. Wani lokaci sai su bada bayani, gurɓataccen bayani, dangane da mu. To amma idan Allah ya ba mu wannan dama mu ka koya wa mutanen mu faɗin labaran mu da kan mu cikin harshen su, to ina tabbatar da cewa za a samu canjin tunani nesa ba kusa ba.
“Ba wai mu a karan kan mu ba Hausawa, a’a, ga dukkanin waɗanda za su fahimci Hausa za su san ya ya Hausawa su ke kan wanda tafarki su ke gudanar da rayuwar su.”
A ƙarshe, ya yi kira ga ‘ya’yan ƙungiyar da su ba su haɗin kai wajen gina tare da samun cigaban ƙungiyar.

Shugabannin da aka rantsar su ne:
1. Tijjani Muhammad Musa – Shugaba;
2. Maimuna Sani Idris Beli – Mataimakiyar Shugaba;
3. Bazul Idris Yaƙub – Sakatare;
4. Abdullahi Lawan – Sakataren Kuɗi;
5. Ibrahim Muhammad Indabawa – Jami’in Yaɗa Labarai da Harshen Hausa;
6. Aliyu Muhammad – Jami’in Yaɗa Labarai da Harshen Turanci;
7. Ɗanladi Zakariya Haruna – Ma’aji
8. Hajiya Sadiya – Mai Binciken Kuɗi ta 1;
9. Abba Shehu – Mai Binciken Kuɗi na 2;
10. Hassan Gama – Mashawarci kan Shari’a;
11. Dakta Murtala Uba – Mashawarci;
12. Rufaida Umar – Mashawarciya;
13. Zahraddeen Ibrahim Kalla – Mashawarci;
14. Yasir Ibrahim Kalla – Mashawarci.
Taron ya samu halartar shaihunan jami’a, malamai da kuma marubuta. Sun haɗa da Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo, Farfesa Faruq Sarkin Fada, Farfesa Hamisu Darma, Dakta Ibrahim Bichi, Dakta Murtala Ahmad, Dakta Bala Muhammad, Dakta Tijjani Almajir, Dakta Isma’il Bala, Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, Hajiya Balaraba Ramat Yakubu, da sauran jama’ar gari da dama.


