KOTUN Shari’ar Musulunci da ke PRP a Kano ta amince da bayar da belin wani fitaccen mawaƙin yabon Manzon Allah (s.a.w.), Malam Usman Mai Dubun Isa.
Tun a ranar 18 ga Yuli, 2023 aka gurfanar da shi bisa zargin ya ɓata wa wani malami, Sheikh Tijjani Usman Zangon Barebari, suna.
A zaman farko da aka yi kotun ta hana belin sa saboda hango cewa hakan zai iya tayar da hankalin mabiyan malamin.
Sharuɗɗan beli da kotun ta bayar sun haɗa da tilas masu karɓar belin su kasance mazauna Jihar Kano ne; dole guda cikin su ya kasance ma’aikacin gwamnatin Kano ne da kuma ɗan kasuwa cikin manyan kasuwannin da ke Kano; dole mai unguwa ya tabbatar da zaman mawaƙin a unguwar sa, sai kuma sharaɗin kawo shi kotu har zuwa ƙarshen shari’ar, idan kuma ya ƙi zuwa ko ya gudu, to za su yi zaman gidan yari na tsawon wata shida.
Duk da waɗannan sharuɗɗan dai kuma kotun ta ce kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kano zai sanya hannu kan cewa mawaƙin ya amince a kan ba zai ƙara aikata irin laifin da ake zargin sa ba.