• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Kotu ta hana beli ga matasan da ake zargi da yin zamba da ɓatanci da sunan Iman Sani Danja

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
September 20, 2022
in Labarai
1
Hajiya Mansurah Isah da Khadijatul Iman Sani Danja

Hajiya Mansurah Isah da Khadijatul Iman Sani Danja

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

KOTUN Majistare mai lamba 47 da ke Kano a jiya ta ƙi ba da beli ga wasu matasa biyu da aka kama bisa zargin su na amfani da sunan jarumar Kannywood Khadijatul Iman Sani Danja su na zambatar jama’a tare da yaɗa batsa a soshiyal midiya.

A jiya Litinin ne dai aka sake gabatar da Jabir Muhammad da Abubakar Sunusi a gaban Mai Shari’a Hadiza Muhammad Hassan bisa tuhumar haɗa kai da ƙirƙirar labarin ƙarya da cin zarafi da kuma ɓata suna.

Jami’in kotun, Auwal Abdullahi, ya karanto masu laifin su tare da bayyana cewa abin da su ka yi ya saɓa wa sashe na 97 da na 324 da na 393 da kuma na 392 na kundin Final Kod.

To amma dukkan su sun musanta zargin.

Lauyar gwamnati mai gabatar da ƙara, Barista Asma’u T. Gwarzo, ta buƙaci kotu da ta ba su wata ranar domin a sake gabatar da su, kuma a nan take kotun ta amince, inda ta aika da su zuwa gidan yari inda za su zauna har zuwa ranar 27 ga Satumba, 2022 sannan a sake gabatar da su.

Mahaifiyar Iman, wadda ƙaramar yarinya ce, wato tsohuwar jaruma Hajiya Mansurah Isah, ita ce ta kai su ƙara a madadin ‘yar ta.

Uwa da ‘ya: Mansurah da Iman

Bayan an fito daga kotun, mujallar Fim ta tattauna da lauyan Mansurah ɗin, wato Barista Rabi’u Sidi, inda ya bayyana dalilin shari’ar da kuma inda aka tsaya. Ya ce, “Ni ina tsaya wa Mansurah Isah ne a kan wannan ƙara inda mu ke ƙarar wasu mutane uku, Jabir Muhammad, Abubakar Sunusi, da kuma wani da har yanzu ba a kai ga kama shi ba, dangane da haɗa kai da su ka yi wajen buɗe shafuka na Facebook, Instagram, Twitter da YouTube inda su ka kira shafin da suna ‘Real Iman Sani Danja’ su na saka hotunan batsa, sannan su ka yi amfani da lambobin wayar su su na kiran wasu mutane su na karɓar kuɗaɗe a wajen su a matsayin ita ce. 

“Kuma sai binciken ya nuna an yi wannan abin domin ɓata wa ita Mansurah Isah suna da iyalan ta. Don haka sai ta gabatar da ƙorafi a gaban ‘yan sanda na SIB kuma aka yi bincike aka kamo su.

“A yanzu ga shi an gabatar da su a gaban kotu, duk da cewa sun musa abubuwan da aka caje su da shi Lauyan su ya tashi ya nemi beli a gaban kotu, ta ce ta ɗaga sai ranar 27 za ta faɗi ra’ayin ta ko za ta bayar da belin ko ba za ta bayar ba.

“Don haka mu dai abin da mu ke nema ga kotu ta yi mana adalci a kan wannan shari’ar, domin akwai mutane da dama da su ke amfani da shafuka na manyan mutane su na ɓata musu suna tare da karɓar kuɗaɗe a wajen wasu da sunan su, don haka mu ke so kotu ta yi hukunci don ya zama izna ga wasu.”

Loading

Tags: Abubakar SunusiBarista Asma'u T. Gwarzo.Barista Rabi'u Sidi.ɓatancifake newsFinal KodJabir MuhammadKhadijatul Iman Sani DanjakotuMai Shari'a Hadiza Muhammad Hassan.majistareMansurah Isahremandzamba
Previous Post

Umar Bankaura ya buƙaci addu’ar jama’a saboda matsanancin rashin lafiya da ya ke fama da shi

Next Post

Lamaj ta ƙaryata Sha’ani kan rashin kuɗi a asusun MOPPAN ta Kaduna

Related Posts

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry
Labarai

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry

June 15, 2025
Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake
Labarai

‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

June 11, 2025
Next Post
Hajiya Fatima Ibrahim (Lamaj)

Lamaj ta ƙaryata Sha'ani kan rashin kuɗi a asusun MOPPAN ta Kaduna

Comments 1

  1. Pingback: Kotu ta hana beli ga matasan da ake zargi da yin zamba da ɓatanci da sunan Iman Sani Danja - LastNg

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!