SHUGABAN Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Alh. Isma’il Na’abba (Afakallah), a yau ya yi barazanar zai yi ƙarar jarumi kuma mawaƙi Yusuf Haruna, wanda aka fi sani da suna Baban Chinedu, a kan ya yi masa ƙazafi da ɓata suna.
A safiyar yau Talata ne dai Baban Chinedu ya fitar da wani bidiyo a shafin sa na Facebook inda ya yi iƙirarin cewa wai Afakallah ya cinye kuɗi har naira miliyan biyar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayar domin a yi wa ɗiyar marigayi Rabilu Musa Ɗanlasan (Ibro) hidimar biki a lokacin da za a yi mata aure.
A bidiyon, har wa yau, Baban Chinedu ya nemi al’umma da su taimaka su shiga cikin lamarin domin a ƙwato wa iyalan Ibro haƙƙin su.
Ya kuma nemi malamai da su ma su shigo domin nema wa marayu haƙƙin su da ya ce wai Afakallah ya cinye.
Shugaban hukumar ya ƙaryata zargin.
Afakallah ya umarci lauyoyin sa da su shigo cikin lamarin domin bi masa haƙƙi.
A takardar da lauyoyin su ka aike wa Baban Chinedu, wadda mujallar Fim ta samu kwafe, sun bayyana cewa babu inda Gwamna ya ba Afakallah wannan kuɗi, sannan babu wani mutum da ya ba shi kuɗi don ya kai wa iyalan Ibro da har zai cinye.
Lauya Abdullahi Musa Ƙaraye tare da abokan aikin sa lauyoyin da ke kare Afakallah sun umarci Baban Chinedu da ya sauke bidiyon da ya saka a dukkan shafukan sa na soshiyal midiya, sannan ya sake yin wani bidiyon na bayar da haƙuri tare da ƙaryata kan sa.
Sun ba shi wa’adin awa 24 kacal ya yi hakan tare da gargaɗin cewa idan kuma ya ƙi yin waɗannan abubuwan, to, kotu za ta ɗauki mataki a kan sa.