• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 15, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Kwamishinan Shari’a ya raba faɗan hukumomi a Kano

by DAGA ABBA MUHAMMAD
August 25, 2023
in Labarai
0
Kwamishinan Shari'a (a tsakiya) ya na sasanta shugabannin hukumomin

Kwamishinan Shari'a (a tsakiya) ya na sasanta shugabannin hukumomin

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

KWAMISHINAN Shari’a na Jihar Kano, Barista Haruna Isah Dederi, ya sulhunta wani saɓani tsakanin Kwamishinar Raya Al’adu da Yawon Buɗe Ido ta jihar, Hajiya Ladidi Garko, da  Manajan Daraktan Hukumar Kula da Masu Yawon Buɗe Ido, Alhaji Tukur Bala Sagagi, tare  da Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta jihar, Alhaji Abba  El-Mustapha.

An yi taron sasantawar a babban ɗakin taro na Ma’aikatar Shari’a a Kano.

Haka kuma, an shirya taron ne domin nemo bakin zaren  rashin fahimtar da ke faruwa wajen gudanar da ayyukan da ya rataya a  tsakanin hukumomin biyu a kan masu sana’ar gidajen kallo (viewing centres) da masu gidajen shirya tarurruka (event centres). 

Da farko Dederi ya yi dogon jawabi dangane da haƙƙi tare da ayyukan da su ka rataya a kan hukumomin biyu, inda bayan doguwar tattaunawa tsakanin shugabannin hukumomin biyu aka samu daidaito.

A sama: Abba El-Mustapha tare da Barista Haruna Isa Dederi. A ƙasa kuma shi ne tare da Hajiya Ladidi Garko

El-Mustapha ya ba da shawarar a raba ayyukan gida biyu, inda kowace hukuma za ta ɗauki ɗaya don ta mai da hankali a kan sa, ita kuma Hajiya Ladidi ta yi na’am da wannan shawarar. 

Bisa la’akari da hakan, sai Dederi ya tabbatar da ba wa kowace hukuma aiki ɗaya don ta mai da hankali a kai don cimma nasarar da gwamnati ta sa a gaba.

A yanzu dai Hukumar Tace Finafinan da Ɗab’i ce ke da alhakin kula da ayyukan masu sana’ar gidajen kallo, ita kuma Hukumar Kula da Al’adu da Masu Yawon Buɗe Ido  ke da alhakin kula da ayyukan masu gidajen shirya tarurruka.

Mahalartan taron bayan an gama taron

Shugabannin sun nuna farin cikin su dangane da yadda Ma’aikatar Shari’a ta kawo ƙarshen taƙaddamar tare da samun nasarar da taron ya samu na cimma matsaya.

Loading

Previous Post

Jarumin Kannywood Jamilu Ibrahim ya samu haihuwa ta 5, jaruma Asma’u Sani ta samu ƙarin jika

Next Post

Sabunta rajista: Za mu kauce wa matsalolin baya – Gidan Dabino

Related Posts

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake
Labarai

‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

June 11, 2025
An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
Next Post
Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, MON

Sabunta rajista: Za mu kauce wa matsalolin baya - Gidan Dabino

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!