JARUMIN Kannywood Shu’aibu Idris (Lilisco) ya sha alwashin kula da ‘ya’yan sa da matar sa Zulaihat Ɗalhat ta mutu ta bari, bisa amana.
A yau Litinin ne jarumar ta fim ɗin ‘Illah’ ta cika kwana arba’in cur da rasuwa.
A wani saƙo da ya wallafa a Facebook cikin alhinin rashin matar sa, Lilisco ya ce, “Allahu Akbar kabiran! Allah ya jiƙan ki da rahama, Allah ya sa Aljanna makoma a gare ki mata ta.”
Ya ƙara da cewa, “Yau Monday kin cika kwana arba’in (40 days). Allah ya sada ki da Annabin rahama (S.A.W.), Allah ya yi miki gafara, Allah ya sa can ya fi nan, halin ki na kirki da kika nuna min, Allah ya sada ni da ke a lahira.
“Na yi rashin ki mai ƙauna ta. Ina miki fatan rahama da yardar Ubangiji mahalicci. Kin riƙe min amana, zan riƙe ta ‘ya’yan ki.
“Allah ya gafarta miki. Ina barar addu’ar ku ‘yan’uwa.”
Kamar yadda mujallar Fim ta ba da labari, Malama Zulai ta rasu ne a ranar Laraba, 23 ga Oktoba, 2024, da misalin ƙarfe 2:00 na rana, a asibitin Nassarawa da ke Kano.
Mutuwar ta ta girgiza jama’a matuƙa, ana ta yi mata addu’ar samun rahama.