DARAKTA, jarumi kuma kakakin Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya, (MOPPAN), Malam Al-Amin Ciroma, ya ƙaryata labarin da aka yaɗa a soshiyal midiya a yau da yamma cewa wai yw rasu.
An tsinci wannan labari mai rikitarwa ne a shafin jarumi Sahir Abdoul, wato Malam Ali na cikin shirin ‘Kwana Casa’in’.
Nan da nan labari ya bazu, inda abokan sana’ar Ciroma su ka riƙa kiran waya don tabbatar da labarin.
Cikin ƙanƙanen lokaci labari ya ishe jarumin, inda nan take ya yi gajeren bidiyo a cikin motar sa ya tabbatar wa da mutane cewa labarin ƙanzon kurege ne ake yaɗawa a kan shi.
Ciroma ya ce, “Yan’uwa, na ji abubuwan da ke faruwa a kan wata sanarwa cewa mun gamu da haɗari, kuma na rasa rai na da sauran su.”
Ya ci-gaba da cewa, “To wannan dai a zahiri, ba sai na ce gaskiya ne ko ba gaskiya ba. Mu na fatan Allah ya kare mu daga irin waɗannan matsaloli da ke faruwa, na kutse a waya da sauran su.
“Na kuma gode da addu’o’i da kuma fatan alkhairi.
“Amma ina ƙara kwantar wa mutane hankali, hakan dai ba ta faru ba. Mu sha ruwa lafiya. Assalamu alaikum.”
Mujallar Fim ta nemi jin ta bakin Al-Amin, sai dai bai yi magana mai tsawo ba. Cewa ya yi: “Alhaji Abba ai wannan abu an riga da an saba. Allah dai ya kyauta kawai.”
Tun ba yanzu ba, an sha yaɗa labaran ƙarya irin wannan a kan ‘yan fim. Za a iya cewa kusan duk fitattun ‘yan fim ɗai-ɗai ba a yi wa irin wannan sharrin ba.