AN samu nasara a taron baje-kolin littafin ‘Ɗaukar Fansa’ na Aysha Asas wanda ƙungiyar marubuta ta Mikiya ta shirya domin ‘ya’yan ƙungiya da makaranta littattafan Hausa da ƙungiyoyi da manyan mutane da sauran hukumomi da ma’aikatun gwamnatin da ƙungiyar ta ke hulɗa da su, su zo su sayi littafin da ƙarin naira ɗari a kan farashin shi na kasuwa.
An ƙaddamar da littafin a Kaduna a ranar 7 ga Maris, 2019.
Alhamdu lillahi, kwalliya ta biya kuɗin sabulu! Mikiya ta fito da sabon tsari fil da zai taimaki marubuci a daidai lokacin da kasuwar littafi ta shiga irin wani surƙuƙi.
Wannan hanya ta yi tasiri sosai wajen yin kasuwancin littafin, domin tun lokacin da aka yi sanarwar mutanen da su ka aiko da kuɗin su ta asusun banki daga jihohi da garuruwa mabanbanta tabbas su na da yawa, musamman ma mutanen Sokoto da Adamawa.
Kamfanin ‘A.S. Creative Writing & Translation Agency’ kawai sun shaida mana an tura masu da kuɗin kwafen littafi 123 wanda kuɗin su ya kama N51,500. Sai kuma waɗanda aka tura ta asusun banki na mawallafiyar, wato ‘yan’uwa da abokan arziki su ka yi mata kara, su ka tura mata da kuɗin kwafe 130 amma kwafe guda-guda su ke buƙata, inda kuɗin ya kama N65,000 daidai.
√ Jinjinar ban-girma ga JRTV da babban daraktan gidan talbijin da rediyon ya sayi kwafe 40 N20,000 amma kwafe biyu ya amsa. Bugu da ƙari ya saya wa ma’aikatan sa da ya zo da su aiki wurin kwafe ashirin, N10,000 amma su ka amshi kwafe biyar.
√ Sai kuma Masarautar Zazzau da su ka sayi kwafe ɗari a kan N50,000. Chiroman Shantalin Zazzau ne ya wakilci masarautar.
√ Aminiyar mawallafiya, wato Aunty Sadiya Kaduna, ta sayi kwafe a kan N10,000 amma kwafe ɗaya ta ce ta ke buƙata.
√ Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kaduna, ƙarƙashin jagorancin mai girma Kwamishina Dakta Usman Muhammad Maƙarfi, sun turo da kuɗin kwafe ɗari ta asusun banki N50,000. Sai kuma ofishin PRO waɗanda abokan hulɗar mu ne sosai su ma sun turo da kuɗin kwafe goma sha biyar (N7,500) a daidai lokacin da ake gudanar da baje-kolin littafin.

√ Ƙungiyar ‘Mikiya Hausa Writers’ ta sayi kwafe 35 da za ta ajiye a ɗakin karatun ta, wanda ya kama N17,500, bayan kuma kowannen ɗan ƙungiya ya sayi adadin kwafe na ƙashin-kai.

√ Hukumar Kula da Ingancin Karatu da Makarantu na Jihar Kaduna, wanda wakilin su ya yi sharhin littafin, sun sayi kwafe 40 a kan N20,000 a ƙarƙashin jagorancin babbar daraktar ma’aikatar, Hajiya Umma K. Ahmad, tare da yi mana wani albishir mai daɗi.
√ Godiya da jinjina mai tarin yawa ga mai girma Hakimin Kurmin Mashi bisa ga shawarwarin sa. Haƙiƙa sun zauna a zukatan mu.
√ Kai, har zan rufe ban faɗi adadin kwafen da kamfanin ‘Mudassir & Brothers’ su ka saya ba bayan mun tashi daga taron. Sun turo da kuɗin kwafe 70 (N35,000) domin rarraba wa ma’aikatan su.
√ Ba za mu manta da kamfanin ‘A.S. Creative Writing & Translation Agency’ ba, wanda shi ne ya ɗauki nauyin Gasar Auna Fahimta a kan littafin, amma duk da haka sun sayi kwafe ɗari da hamsin (N75,000).
√ Mu na yi wa ƙungiyoyin da su ka halarci taron baje-kolin, musamman Majalisar Gobe Da Labari na gidan DITV/Alheri Radio, Kaduna, godiya, da kuma sauran makaranta da marubuta da su ka zo domin sayen littafin. Haƙiƙa kun nuna mana karamci kuma kwalliya ta biya kuɗin sabulu har da na turaren fesawa.
Littafin ‘Ɗaukar Fansa’ ya shiga rukunin littattafan Hausa da su ka shiga kasuwa cikin nasara.
Ƙungiyar ‘Mikiya Hausa Writers’ ta fito da sabon salon da zai taimaka sosai don farfaɗo da kasuwancin littafi. Jinjina a gare ku kafatanin ‘ya’yan ƙungiyar Mikiya!
Allah ya shige mana gaba.