A YAU Litinin, 8 ga Yuni, 2020, da yammar nan, Allah ya yi wa mahaifin fitaccen jarumi Ali Nuhu rasuwa.
Mista Nuhu Poloma ya rasu a Gombe sakamakon gajeren rashin lafiya da ya yi.
Iyalin sa sun faɗa wa mujallar Fim cewa shekarun sa 79 a duniya.
Mista Poloma tsohon ma’aikaci ne a hukumar Kwastam ta Nijeriya, sannan ya taɓa zama ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Tangale da Waja a Jihar Bauchi a ƙarƙashin jam’iyyar NPN kafin a ba Gombe jiha.
Bugu da ƙari, ya taɓa zama shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Gombe.
A cikin ‘ya’yan sa akwai Kiristoci da Musulmi.
Ya auri mahaifiyar Ali Nuhu, Hajiya Fatima, a Kano. Ita ta jima da rasuwa.
Allah ya ba jarumi Ali Nuhu da ‘yan’uwan sa haƙurin rashin mahaifin su, amin.