MAHAIFIN fitacciyar jaruma Hafsat Idris (‘Ɓarauniya’) ya kwanta dama.
Alhaji Idris Ahmad, mai kimanin shekaru 75 a duniya, ya rasu a safiyar yau Asabar, 7 ga Disamba, 2019 a Asibitin Malam Aminu Kano da ke Kano.
Kafin rasuwar sa, ya daɗe ya na fama da rashin lafiya, wanda ashe ciwon ajali ne.
Marigayin ya yi dukkan jinyar sa a nan asibitin na Malam Aminu Kano.
An yi jana’izar sa a gidan sa da ke garin Kura da ke Jihar Kano, inda nan ne mahaifar sa.
Hafsat da kan ta ce ta fara bada sanarwar wannan babban rashin a soshiyal midiya, inda ta ce: “Inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un! Allah ya yi wa mahaifi na rasuwa. Ina roƙon Allah ya yi mashi rahama, ameen.”
Ta haɗa da alamu masu bayyana tsananin zubar hawaye.
A tare da sanarwar akwai wani hoto da Hafsat ɗin ta ɗauka tare da mahaifin nata a asibiti, ta dafa kafaɗun sa, kuma ga hawaye na zuba daga idanun ta.
Da yake wasu sun yi zaton ko gawar mahaifin nata ta rungume ta yi hoton, daga baya ta koma soshiyal midiya ta tura da wani saƙon mai cewa, “Na yi ‘posting picture’ tare da mahaifi na, wasu na cewa wai na yi hoto da gawa. Ya za a yi hoto da gawa? Ban yi hoto da gawa ba. Wannan ‘picture’ tun da rayuwan shi mu ka ɗauka. Allah ya mishi rahma, ameen.”
To, mu na addu’ar Allah ya jiƙan sa da rahama, ya kuma albarkaci dukkan abin da ya bari.