A WATAN Yuni, 2020, Mai Girma Sarkin Kudun Katsina, Alhaji Muhammadu Tukur Bature, ya cika shekara 28 da naɗawa, domin muwa a ranar 4 ga Yuni, 1992 ne, da ƙarfe 10:30 na safe, Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Muhammadu Kabir Usman, ya naɗa shi a matsayin Sarkin Kudun Katsina na Farko (1) kuma Hakimin Gundumar Ɗanja na Biyu (2), a fadar Mai Martaban da ke Katsina.
Shi dai Alhaji Muhammadu Tukur Bature (wanda ake kira Alhaji M.T. Bature), ɗa ne ga Alhaji Mu’utasimu Ibrahim Nadabo, Iyan Katsina (1953 – 1956) kuma jika ga Alhaji Tukur Ramalan, Makaman/Iyan Katsina, Hakimin Gundumar Ɗanja/Bakori na Farko (1914 – 1953).
An haifi Alhaji M.T. Bature, Sarkin Kudun Katsina, a shekarar 1938 a garin Bakori.
Ya fara karatun Alƙur’ani a makarantar Liman M. Ahmadu, kuma ya yi karatun elemantare a garin Bakori daga shekarar 1945 zuwa 1948. Haka nan kuma ya yi karatun Makarantar Midil ta Katsina (1949 – 1952), da sakandare a St. Paul’s College, Zariya, wadda yanzu ake kira Kufena College, daga 1952 zuwa 1959.
Alhaji M.T. Bature ya yi karatun Higher School Certificate (HSC) a Keffi da King’s College, a Legas. Ya kammala digiri ɗin shi a fannin Shari’a (LLB) a Jami’ar London (1963 – 1966.
Da ya dawo gida Nijeriya a 1966, sai ya fara aiki a Ma’aikatar Ilimi, a ƙarƙashin Interim Common Services Agency (ICSA).
Ya kuma riƙe Mataimakin Sakatare (Cabinet and Security) na Jihar Kaduna. A lokacin kuma (1968) aka ƙara masa da kula da tare da tattara kuɗin maniyyata aikin hajji. A wannan shekarar ne ya yi aikin hajjin sa na farko.
Haka kuma ya shugabanci sashen harkokin cikin gida (Internal Affairs Division) kafin ya zama ma’aikata (wato Ministry) mai cin gashin kan ta.
A dai wannan shekarar ta 1968, sai ya koma da aiki a kamfanin jiragen sama na Nijeriya (Nigeria Airways). A nan ya riƙe waɗannan muƙaman:
– Company Secretary
– Deputy Director, Administration
– Director, Administration
– Managing Director/Chief Executive Officer.
Ya yi ritaya daga aiki a shekarar 1983.
Haka nan kuma ya riƙe waɗannan muƙamai:
– Member, Special Presidential Task Force on Economic Matters a zamanin Jamhuriya ta Biyu (1981 – 1983)
– Commissioner for Economic Development a 1976 (on Secondment)
– Chairman, State Development Plan Implementation Committee, Kaduna State
– Chairman, State Tenders Board, Kaduna State
– Chairman, Kaduna State Manpower Board
– Chairman, Solidarity Packaging Company, Lagos
– Member, Katsina State Judicial Service Committee (1985 – 1992)
– Member, Katsina State Civil Disturbance Tribunal
– Member, Advisory Committee, Gidauniyar Jihar Katsina (1990 zuwa yau)
– A cikin 1992 aka naɗa shi Sarkin Kudun Katsina, Hakimin Ɗanja.
A ƙarƙashin jagorancin sa, Ƙaramar Hukumar Ɗanja ta samu gagarumin cigaba ta fannonin ilimi, lafiya, sana’o’i, kasuwanci, noma, kiwo, hanyoyi, buɗe bankuna, da kuma bunƙasa hanyoyin rayuwar jama’a da inganta sha’anin tsaro.
Ya na da mata da ‘ya’ya biyar – maza biyu, mata uku.
Ya yi aikin hajji sau 10. Haka kuma ya zagaya duniya; kusan ba ƙasar da bai je ba.
Addu’ar mu ga Sarkin Kudun Katsina ita ce: Allah (SWT) ya ja zamanin ka, ya ƙaro tsawancin kwana mai albarka, ya ƙara ba ka lafiya amintacciya, kuma ya albarkaci iyali, amin.
* Alhaji Yazidu shi ne Sarkin Fulanin Ɗanja