A JIYA Talata, 17 ga Fabrairu, 2020 wani mai fafutikar kare haƙƙin ɗan’adam ya maka mawaƙi Ibrahim Ahmad Rufa’i (Deezell) a Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna bisa zargin sa da ɗaukar bidiyon tsiraici na Maryam Booth tare da yaɗa shi don ya zubar mata da mutunci a idon duniya.
Mutumin, mai suna Muhammad Lawal Gusau, wanda ba a san ko wanene ba, ya buƙaci kotun da ta tilasta wa Deezell biyan jarumar diyyar naira miliyan goma.
Waɗannan bayanai na ƙunshe ne a cikin takardar ƙara wadda shi Muhammad Lawal Gusau ya shigar a kotun, wadda mujallar Fim ta samu kwafi.
Idan ba ku manta ba, bayan fitar guntun bidiyon da ake ta ce-ce-ku-ce a kai, Deezell ya ƙaryata zargin da ake masa na yaɗa bidiyon, a yayin da ita kuma Maryam ta yi iƙirarin cewa lallai shi ne ya ɗauki bidiyon.
Ta ƙara da cewa lamarin ya faru ne shekaru kusan uku da su ka gabata a lokacin da ta ke soyayya da shi.
Deezell ya yi alƙawarin zai yi ƙarar Maryam idan har ba ta ba janye zargin ta a kan sa ba kuma ta ba shi haƙuri.
Ya cika wannan alƙawarin, ya maka ta ita da wasu mutane biyar a Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar 10 ga Fabrairu, 2020.
Wannan ƙarar da aka kai shi a Kaduna tamkar martani ne ga tasa ƙarar.