• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 16, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Mai’unguwa Sani Mu’azu ya yi wa abokan gaba raddi

by DAGA IRO MAMMAN
July 19, 2020
in Labarai
0
Alhaji Sani Mu'azu

Alhaji Sani Mu'azu

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
AN naɗa fitaccen jarumi Alhaji Sani Mu’azu sarautar Mai’unguwa na unguwar da ake kira Ali Kazaure da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, cikin garin Jos, babban birnin Jihar Filato.
 
Kafin naɗin nasa, shi ne Galadiman unguwar.
 
Wata majiya ta shaida wa mujallar Fim cewa sabon mai’unguwar ya yi takara mai zafi da wasu masu neman sarautar kafin Allah ya sa jama’a su zaɓe shi.
 
Sani Mu’azu mutum ne wanda ya bada gagarumar gudunmawa a unguwar, inda ya kan yi faɗi-tashi don kyautata zamantakewa a tsakanin jama’ar unguwar da ma na Jos baki ɗaya.
 
A fagen sana’ar fim kuma babba ne, domin ya na daga cikin manyan jagororin masana’antar finafinan Hausa ta Kannywood.
 
Sani, wanda furodusa ne kuma darakta, shi ne shugaban kamfanin harkar fim na Lenscope Media Limited, Jos.
 
Shi ne shugaba na farko da ya jagoranci uwar ƙungiyar masu harkar finafinan Hausa, wato Motion Picture Practitioners Association of Nigeria (MOPPAN).
 
Ficen sa ya ƙaru a wajen masu kallo cikin ‘yan watannin nan saboda fitowar sa a matsayin Gwamnan Jihar Alfawa a shirin diramar ‘Kwana Casa’in’ na gidan talbijin na Arewa24.
 
Ban da rawar da ya ke takawa a Kannywood, ya kan kuma fito a finafinan kudu, wato na Nollywood.
 
A saƙon murnar zaɓen sa da aka yi, wanda ya tura a soshiyal midiya a daren yau, Sani Mu’azu ya yi godiya ga Allah da kuma waɗanda su ka zaɓe shi, sannan ya yi raddi mai zafi ga mutanen da su ka nemi hana ruwa gudu a takarar sa.
 
Ya rubuta saƙon ne da Turanci, amma mujallar Fim ta fassara shi kamar haka:
 
“Ina farin cikin miƙa godiya ta ga dukkan jama’a masu zaɓe, waɗanda su ka wakilci yankuna uku na Unguwar Ali Kazaure, waɗanda su ka zaɓe ni a matsayin sabon mai’unguwar yankin.
 
“Tare da yardar Allah SWT ne na hau wannan matsayi domin ko kaɗan ban tsara zama hakan ba. Da ma can ina da muƙamin sarauta inda ake damawa da ni cikin al’amuran jama’a.
 
“Na ɗauka cewa ayyukan da ke gaba na sun ishe ni, saboda haka lokacin da aka matsa mani da cewar in shiga wannan takarar, na amince ne ba da ɗoki ba. 
 
“Sai da na roƙi Allah da ya fallasa abokan gaba ta a wannan tafiya to amma, abin mamaki, sai ya musanya abin, ya fallasa abokai na waɗanda ke cike da gaba da ni. 
 
“A cikin ‘yan kwanakin nan, abokai na da mu ka tashi tare tun mu na yara su ne su ƙa riƙa yaɗa ƙarairayi a kan abin da ban taɓa sanin na ce ko na yi ba, su na iƙirarin wai abin ya faru ne shekaru 30 da su ka gabata. Shekaru 30 fa! Kuma wai waɗannan mutanen su na iƙirarin cewa su abokai na ne na kurkusa da ni! Kuma sun kasa yi mani nasiha har tsawon shekara 30, har sai da su ka ji zan zama mai’unguwa. Ko a hakan ma, ba su zo su ka same ni kai-tsaye da ƙaryar su ba, sai su ka tafi wajen waɗanda za su yi zaɓen da nufin su ja hankalin su don kada su zaɓe ni. Wai abokai kenan.
 
“Kuma ina gode wa Allah SWT da ya ba ni ikon mallakar gidaje da gonaki da sauran kadarori, har da inda na ke zaune tare da iyali na. 
 
“Ban san cewar abin da na mallaka ya tsone wa wasu daga cikin abokai na ido ba har sai da su ka shiga baza labaran ƙanzon kurege cewa wai gida na ba nawa ba ne. 
 
“Mallakar kadarori dai ba laifi ba ne kuma bayanin wa ya mallaki abu kaza da kaza ai ba sirri ba ne. A gani na, batun cewa ba ni ne mamallakin abin da na mallaka ba wasan yara ne, domin ai da sai su fara zuwa ma’aikatar ƙasa da safiyo tukuna don su tabbatar da abin da su ke iƙirari a kai. A gaskiya gaba aba ce mara kyau. 
 
“Amma dai an nuna mani so da ƙauna saboda gudunmawa ta ga al’umma. Mutanen da ma ban yi mu’amala mai zurfi da su ba sun tsaya mani, sun jajirce a kai na a yau. Sun yabe ni da ayyuka na matuƙa a bayan ido na, su na faɗin kyawawan abubuwa na waɗanda ma har na manta da su. Na ji daɗi ƙwarai da samun irin waɗannan mutanen, kuma ina gode masu.
 
“A ƙarshe, na yi alƙawarin zan yi aiki tare da kowa da kowa ba tare da tsoro ko nuna bambanci ba. Na sha alwashin zan riƙe kowa bisa gaskiya da adalci. Zan ci gaba da yin aiki don haɓaka cigaban unguwa ta, da ma al’umma baki ɗaya da dukkan ƙarfi na don amfanin kowa da kowa. Na ƙudiri aniyar zan rungumi kowa da kowa ba tare da nuna wariyar ƙabila ko addini ba. Na zama abin da na zama ne saboda ku.
 
“Abokai na, don Allah ku taya ni da addu’a a wannan sabon aiki da aka ɗora mani.”
 
A nan ƙasa, ga jawabin da Sani Mu’azu ya rubuta da Turanci:
 
I sincerely wish to thank all members of the electoral college, representing the three zones in Ali Kazaure Ward, that voted for me as the proposed new ward head of the area.
 
It is the will of Allah SWT that I assume this responsibility because this was not part of my plans in any way. I am already a title holder who is very active in community affairs. I thought that my plate is already too loaded so when I was pressured to offer myself to serve here too, I was very reluctant.
 
I prayed to God to help me expose my enemies in this journey and guess what, God exposed my friends who harboured so much hate against me instead. In these few days, childhood friends spread lies about what I never knew I did or said, claiming it happened some 30 years ago. 30 years! And these people claimed they are friends that are close to me! And they could not admonish me in 30 years, until they heard that I am about to become a ward head. Even then, they did not come to me with their falsehood, they went to members of the electoral college to convince them against me. Friends indeed.
 
I also thank Allah SWT for enabling me to own houses, farms and other properties including where I live with my family. I never knew that what I owned is an issue to some of my friends until they went to town with claims that I don’t own my house. Ownership of properties is a legal thing and information about who owns what is in public space. I find claims that I don’t own what I owned pedestrian as they should have gone to lands and survey to ascertain the veracity of their claims first. Hate is such a terrible thing.
 
But I was shown love and appreciation for my community services too. Folks I never really relate with closely stood for me, stood by me and stood with me at this moment. They poured encomiums on me and my works in my absence, saying good things I can’t even remember happened. These group of people really touched me deeply and I am appreciative of them.
 
In the whole, I pledged to work with all without fear or favour. I promised to be fair and balanced. I will continue to work towards the growth and development of my ward, and the entire community with all my might and for the benefit of all. I undertake to try to carry everyone along irrespective of tribe or religion. I am, because of you all.
 
Friends, please pray for me in my new assignment.

Loading

Previous Post

Abida Muhammad ta haifa wa soja Al-Mustapha mai sunan sa

Next Post

Matan da ke son aure na sun fi dubu, inji Ɗantani Maishayi na cikin ‘Daɗin Kowa’

Related Posts

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry
Labarai

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry

June 15, 2025
Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake
Labarai

‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

June 11, 2025
Next Post
Jarumi Murtala Alasan ya yi shigar Ɗantani Maishayi

Matan da ke son aure na sun fi dubu, inji Ɗantani Maishayi na cikin 'Daɗin Kowa'

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!