MAKARANTAR nan ta koyar da harshen Turanci, Jammaje Academy, ta naɗa jarumin Kannywood, Ahmadu A. Adamu, wanda aka fi sani da Daddy Hikima ko Abale a cikin shirin ‘A Duniya’, matsayin jakaden ta na musamman.
An yi wa jarumin wannan naɗin ne a wajen taron duniya da makarantar ta shirya a ranar Laraba, 21 ga Disamba, 2022 mai taken ‘Jammaje International Day’ a ɗakin taro na Meena Events Centre da ke Titin Lodge cikin unguwar Nasarawa a birnin Kano.
A cikin jawabin sa, Shugaban makarantar, Malam Kabiru Musa Jammaje, ya bayyana cewa manufar taron ita ce a ƙarfafa wa matasa gwiwa da zaburar da su a kan neman ilimi da sana’o’i don dogaro da kai.
Jammaje, wanda babban furodusa ne a Kannywood, ya ce hakan ne ya sa baya ga koyar da Turanci, makarantar ta samar da wani aji domin koyar da dabarun harkar fim ga matasa, kuma tuni aka fara yaye ɗaliban da aka koyar.

Shi ma da ya ke nasa jawabin, babban baƙo a wajen, Farfesa Mustapha Ahmad Isa, ya bayyana cewa irin ƙoƙarin da Jammaje ya ke yi na samar da cigaba ga rayuwar matasa abin a yaba ne.
Dangane da jakadancin da aka bai wa Abale kuwa, cewa ya yi: “Wannan makarantar ta matasa ce da ta ke koyar da matasa karatu da kuma sana’o’i, musamman abin da ya shafi harkar fim, kuma kasancewar Abale matashi kuma ɗan fim da ya ke da ɗimbin jama’a mu ka ga dacewar sa da ya zama jakaden wannan makaranta ta ‘Jammaje Academy’.
Ya ƙara da cewa, “Idan aka duba, shi Malam Kabiru Musa Jammaje matashi ne kuma ya damu da rayuwar matasa, inda ya bayar da lokacin sa wajen koyar da su Turanci, sannan ya zuba kuɗin sa a cikin harkar fim ya yi finafinai da dama, sannan ya zo ya ke koyar da yadda za a yi fim ɗin. Wannan ba ƙaramin aiki ba ne, kuma ya kamata a jinjina masa.
Ya buƙaci matasa da su yi koyi da irin waɗannan ayyukan da Jammaje ya ke yi domin a samar da cigaban rayuwa ga matasan mu na yanzu da kuma masu zuwa nan gaba.

Taron ya samu halartar ‘yan fim da mawaƙan masana’antar Kannywood. Mawaƙa Mudassir Kasim da Salisun Fati da Abdullahi Amdaz sun gabatar da waƙoƙi a wajen.