SHUGABAR gidauniyar nan ta tallafa wa mabuƙata da marasa lafiya mai suna ‘Today’s Life Foundation’, Hajiya Mansurah Isah, ta bayyana cewa irin matsalolin da ta ke cin karo da su wajen aikin agaza wa jama’a sun sa wani lokacin sai ta ji kamar ta dakatar da wannan fafutikar, iyakacin abin da ta yi kawai Allah zai dubi zuciyar ta ya ba ta lada.
Fitacciyar tsohuwar jarumar ta finafinan Hausa ta bayyana haka ne a lokacin da ta ke tattaunawa da mujallar Fim kan irin nasarorin da gidauniyar ta ta samu tun daga lokacin da aka kafa ta.
Mansurah, wadda matar fitaccen jarumi kuma mawaƙi Sani Musa Danja ce, ta ce a gaskiya an samu nasara sosai, domin kuwa a tsawon lokacin da ta samar da gidauniyar zuwa yanzu akwai ɗimbin mutane da su ka amfana da ita.
“Duk da dai tun kafin na samar da wannan gidauniyar na daɗe ina tallafa wa jama’a, amma da na kafa wannan gidauniyar abin ya fi tsari kuma mabuƙata sun fi cin gajiyar abin fiye da lokacin da na ke yi a baya,” inji ta.
Ta ƙara da cewa: “Don haka a yanzu zan iya cewa mun samar wa da mutane da yawa, musamman mata, hanyoyin dogaro da kai ta hanyar koya masu sana’o’i da ba su jari.
“Kuma mu na da ɓangare na samar wa mabuƙata abinci wanda aka dafa ko kuma tsaba.
“Wannan ƙoƙarin mun yi shi a cikin birni da ƙauyuka, duk mu na shiga domin kai wa mabuƙata kayan tallafi.
“Baya ga haka, mu na shiga asibitoci domin kai wa marasa lafiya magani da kuɗin da za su ɗan riƙe a hannun su, kamar ɓangaren mata masu haihuwa da ƙananan yara.
“To irin haka dai mun samu nasarori sosai kuma har yanzu a kan haka mu ke, don haka ne ma kullum a kan je gida ko a kan hanya a tare ni domin gabatar mini da buƙatar mara lafiya, abin da na ji zan iya sai na yi, wanda kuma na ji ba zan iya ba sai na nemi gudunmawar mutane da su ke son tallafawa.”
Da ta juya ɓangaren irin matsalolin da ta ke cin karo da su a cikin gudanar da wannan aikin, sai malamar ta ce, “Har ga Allah babu abin da ya fi zame mini matsala kuma ya ke jefa ni cikin tashin hankali kamar a samu mutum cikin yanayi na buƙatar a ceto rayuwar sa, amma sai ka ga wani ana cikin haɗa kuɗin da za a yi masa magani sai Allah ya karɓi ran sa. Wannan abin ya na tayar mini da hankali!
“Wani kuma sai ka samu an haɗa kuɗin an je an ɗauki tsawon lokaci ana ta magani, ƙarshe sai Allah ya karɓi ran sa.
“Wata kuma matsalar da ta fi tayar mini da hankali ita ce mutum ya zo da rashin lafiyar sa, an nemi kuɗi don a yi masa magani, sai ya ce shi ba haka ya ke so ba. Misalin da zan ba ka shi ne akwai wata yarinya da ta ke fama da ciwon daji a hannun ta, mu ka yi ta fafutikar haɗa kuɗin da za a yi aikin kuma daga ƙarshe dai an samu, mu ka je asibiti za a yi aikin, sai likitan ya ce sai dai a yanke mata hannun in dai ana so ta samu lafiya.
“Amma abu mafi tashin hankali, sai iyayen ta su ka ce ba su yarda a yanke mata hannu ba. To ba yadda mu ka iya, sai mu ka haƙura, tunda ‘yar su ce.
“To irin wannan tashin hankali sai wani lokacin na rinƙa tunanin ko dai na haƙura da wannan abin? Amma dai har yanzu ina nan ina ci gaba.”
Daga ƙarshe, Mansurah Isah ta yi kira ga masu wadata da su rinƙa shiga asibiti ko wasu wurare da ake buƙatar taimako su ga yadda al’ummar Annabi su ke cikin wani yanayi na buƙatar taimakawa.
