• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 15, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Mansurah ta jima da barin gidan Sani Danja, inji majiya

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
May 27, 2021
in Labarai
4
Mansurah ta jima da barin gidan Sani Danja, inji majiya
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

* ‘Aure Sani ya yi a asirce’

FITACCIYAR jaruma Mansurah Isah ta daɗe da tarewa a gidan hayar da ta kama a Kano bayan tsinkewar igiyar auren ta da Sani Musa Danja, wata majiya ta faɗa wa mujallar Fim a yau.

Labarin da ake yaɗawa cewa auren jaruman biyu na Kannywood ya mutu ya na ci gaba da bazuwa a tsakanin ‘yan fim da sauran jama’ar gari, amma dai su jaruman sun ƙi cewa uffan a kai.

Shirun da su ka yi ya ƙara iza wutar ji-ta-ji-tar.

Tsofaffin jaruman dai sun yi aure ne a cikin 2007, kuma sun haifi ‘ya’ya huɗu – mace ɗaya (Khadijatul Iman) da maza uku (Khalifa Sani, Yakubu da Yusuf).

A ji-ta-ji-tar da ake yaɗawa, an ce wai Mansurah ta wallafa wani saƙo a Instagram jiya da dare, inda ta bayyana cewa a yanzu babu aure tsakanin ta da Sani.

An ce bayan minti ɗaya sai ta goge rubutun ba tare da ta bada dalili ba.

Sai dai kuma mujallar Fim ta tambayi ‘yan fim da dama su nuna mata hoton saƙon da aka ce ta wallafa ɗin, wato ‘screenshot’, amma babu wanda ya ke da shi.

Labarin mutuwar auren ya haifar da surutai a guruf-guruf na ‘yan fim da kuma wasu wurare na soshiyal midiya tun daga jiyan.

Mujallar Fim ta so jin ƙarin bayani ta bakin jaruman biyu, amma ba su amsa waya ba. Haka kuma ba su amsa saƙon tes da mujallar ta tura musu na neman gaskiyar labarin ba.

Sani Danja da Mansurah Isah

Wata majiya ta kurkusa da Mansurah ta shaida wa mujallar Fim cewa auren ya jima da mutuwa, kawai faɗa ne ba a yi ba.

 “Auren Sani da Mansurah Isah ya daɗe da mutuwa. Har Mansurah ma ta kwashe kayan ta daga gidan Sani, ta koma gidan hayar da ta kama,” inji majiyar. “Sun riƙa nuna wa mutane kamar su na tare.”

Majiyar ta ƙara da cewa Mansurah ta koma gidan ne tare da ‘ya’yan ta, kuma ta sha alwashin ba za ta taɓa ba Sani ɗan ta ya riƙa ba.

Wata majiyar ta daban kuma ta sanar da wakilin mu cewa auren tsohuwar jarumar da fitaccen jarumar ya girgiza ne lokacin da ya ƙara aure.

Majiyar ta ce, “Shakka babu, Sani ya yi aure a asirce a Kaduna, kuma matar ma ta haifi ɗa namiji.”

Ta ƙara da cewa Mansurah ba ta san da auren ba har zuwa lokacin da aka yi haihuwar.

To amma binciken da Fim ta yi a Kaduna bai samu tabbacin wannan auren da aka ce Sani ya yi ba.

An faɗa wa wannan mujallar cewa ba wannan ba ne karo na farko da Sani ya saki Mansurah.

“Ya taɓa sakin ta a lokacin da su ke zaune a unguwar Karu a Abuja, daga baya aka sasanta su,” inji mai ba mu labarin.

Mai ba mu labarin ta ce Mansurah ta gaji da halayen Sani ne na rashin kula da iyali. “Ita ke komai a gidan, har da ciyarwa,” inji majiyar. “Mansurah mace ce mai ƙoƙarin neman abin rufa wa kan ta da iyalin ta asiri.”

Wakilin mu ya lura da cewa jaruman biyu kan wallafa hotunan su tare da ‘ya’yan su a soshiyal midiya a lokacin bukukuwan Sallah, amma a bana ba su yi hakan ba. Mansurah ta wallafa hotunan ‘ya’yan ne su kaɗai, shi kuma Sani ya wallafa hotunan da ya ɗauka shi da abokin sa Yakubu Muhammad da kuma ‘ya’yan a ranar Sallah.

Rabon da Mansurah ta wallafa hotunan mijin nata tun cikin Janairu 2021 lokacin da ta tura hotunan sa na tallar kamfanin Maggi. Ita jakada ce ta kamfanin, inda biyan ta maƙudan kuɗaɗe.

Mansurah dai ta na ci gaba da aikin ta na tallafa wa mabuƙata a ƙarƙashin gidauniyar ta mai suna ‘Today’s Life Foundation’.

Mutuwar auren ta ta nuna cewa ‘tagwayen’ kamfanin 2-Effects Empire, wato Sani Danja da jarumi Yakubu Muhammad, duk sun rabu da matan su da su ka wanka a auren fari.

Yakubu ya shafe shekaru masu yawa tun da ya saki Sadiya, ɗiyar fitacciyar jaruma Hajiya Zainab Musa Booth kuma yayar jaruma Maryam Booth.

Sun haifi ‘ya ɗaya mai suna Nadiya, kuma har yanzu Yakubu bai yi wani auren ba.

Sani Danja (a dama) da ‘ya’yan sa tare da aminin sa, Yakubu Muhammad, a ranar Ƙaramar Sallah da ta gabata

Loading

Tags: 2-Effects EmpireAuren Sani Danja da MansurahKannywoodMansurah IsahSani Musa Danja
Previous Post

INEC ta bayyana yadda sabon injin rajista ke aiki

Next Post

Abba, Editan mujallar Fim, zai angwance a ranar 4 ga Yuni

Related Posts

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake
Labarai

‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

June 11, 2025
An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
Next Post
Abba, Editan mujallar Fim, zai angwance a ranar 4 ga Yuni

Abba, Editan mujallar Fim, zai angwance a ranar 4 ga Yuni

Comments 4

  1. Asma'u. says:
    4 years ago

    Subbuhanallah! amma gaskiya banji dadi ba sbd al’arshi nata girgiza’ a duk lokacin da akasa mu’ muwar aure, muwar aure baya haifar da alkhairi a duniya. Dan Allah duk abunda kukeji azuciyoyin mu toh ku aje shi, kusa santa, sbd rayuwan yaran ku. pls! ai ita rayuwa dole sae ansa hakuri agaba, sannan zata tafi dai dai.

  2. Auwalu sidi says:
    4 years ago

    Gaskiyar magana wlh banyi farin cikin hakanba, domin aurensu yana daya daga cikin auren soyayarda nayi alfahari dashi, kuma nake gurin samun soyayyata aure irintasu, wlh kullum burina nakasance da macenda zata soni kuma tanayin alfahari dani kamar yanda naga mansura tana yiwa sani danja. Shawara dan Allah, idan aurenku yana gyaruwa ku gyara, ko dan yaranku.

  3. Hamida Muhammad says:
    4 years ago

    Subhanallah.Allah yadaidaita tsakaninku

  4. Bala Tasiu says:
    3 years ago

    Comment:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!