ALLAH ya yi wa shahararren marubucin nan, ɗan siyasa kuma ɗan kasuwa, Alhaji Bashir Othman Tofa, rasuwa.
Alhaji Bashir Tofa ya rasu a safiyar yau a asibiti a Kano bayan ya yi fama da rashin lafiya na wani gajeren lokaci.
Shekarun sa 75 a duniya.
A ƙarshen makon nan da ya gabata an yi ta yaɗa ji-ta-ji-ta a soshiyal midiya cewa ya rasu, amma a lokacin Allah bai ɗauki ran sa ba, ya na dai cikin zafin ciwo.
Wata majiya ta faɗa wa mujallar Fim cewa a jiya an saka shi cikin na’ura mai bada iskar shaƙa (ventilator) saboda ciwon nasa ya ta’azzara.
Shi dai marigayi Bashir Tofa, an fi sanin sa a matsayin wanda ya yi takarar zama shugaban ƙasa a lokacin Jamhuriya ta Uku, wato zamanin gwamnatin mulkin soja ta Janar Babangida.
A lokacin ne ya yi takarar a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar NRC, su ka gwagwata shi da Alhaji MKO Abiola na jam’iyyar SDP. A ƙarshe, Abiola ya ci zaɓen, amma kuma gwamnatin soja ta soke zaɓen na 12 ga Yuni, 1993.
An haifi Alhaji Bashir Tofa ne a Kano a ranar 20 ga Yuni, 1947. Ya yi karatu a Ƙaramar Makarantar Firamare ta Shahuci da Babbar Makarantar Firamare ta cikin Birni duk a Kano, sannan daga 1962 zuwa 1966 ya yi karatu a Kwalejin Lardi da ke Kano.
Alhaji Bashir ya yi aiki a kamfanin inshora na ‘Royal Exchange Insurance Company’ daga 1967 zuwa 1968, sannan ya tafi London ya yi karatu a ‘City of London College’ daga 1970 zuwa 1973.
Tofa ya shiga harkar siyasa a cikin 1976 inda aka zaɓe shi kansila mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa. Bayan shekara ɗaya kuma aka zaɓe shi memba a Majalisar Tsara Kundin Tsarin Mulki (Constituent Assembly) wadda ta tsara Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1979.
A zamanin Jamhuriya ta Biyu, ya zama Sakataren jam’iyyar NPN, daga baya kuma ya zama Sakataren Kuɗi na ƙasa na ita jam’iyyar.
A zamanin Jamhuriya ta Uku kuma da shi aka kafa ƙungiyar siyasa mai suna ‘Liberal Movement’ wadda ta rikiɗa ta zama ‘Liberal Convention’.
Da gwamnatin mulkin soja ta ƙi yi wa ‘Liberal Convention’ rajista, ta ƙirƙiro jam’iyyu biyu, wato SDP da NRC, sai Tofa ya shiga NRC a cikin 1990, wanda a ƙarshe ya zama shi ne ɗan takarar zama shugaban ƙasa na jam’iyyar.
Ya ci gaba da kasancewa jagora kuma dattijo a siyasar Jihar Kano da ma Arewa har zuwa ƙarshen rayuwar sa.
Haka kuma ya ci gaba da gudanar da harkokin sa na kasuwanci, inda shi ne ciyaman na wani kamfanin hada-hadar man fetur mai suna ‘International Petro-Energy Company’ (IPEC) da kuma kamfanin ‘Abba Othman and Sons Ltd’.
Tofa zaƙaƙurin marubuci ne wanda ya wallafa littattafan hikaya masu yawa, da kuma wani littafi kan kimiyyar da ke cikin Alƙur’ani mai tsarki.
Bugu da ƙari, ya kasance uba kuma mashawarci ga ƙungiyoyin marubuta daban-daban.
Ya rasu ya bar matan sa da ‘ya’yan sa da kuma dangi da masoya masu yawan gaske.
Allah ya rahamshe shi, amin.