SANANNEN marubucin nan kuma mashiryin finafinai, mazaunin Zariya a Jihar Kaduna, Malam Abdullahi Yahaya Maizare, a yau ya samu kuɓuta daga hannun ɓarayi masu garkuwa da mutane.
Hakan ya biyo bayan kuɗin diyya da iyalan sa su ka biya ɓarayin da ke riƙe da shi.
Majiyar mujallar Fim ta ce a yau Talata aka tsince shi magashiyan a wani wuri, amma majiyar ta shaida wa mujallar cewa ba ta san inda aka tsince shi ɗin ba domin a lokacin da iyalin sa su ka kira ta ba ta jin su sosai, domin su na ta kuka.
Sai dai matar sa ta ce ya dawo ba shi da lafiya, don ko magana ba ya iya yi, har an kwantar da shi a asibiti.
Idan kun tuna, a makon jiya mujallar Fim ta ba ku labarin yadda ɓarayin su ka sace Maizare a daren Asabar, 7 ga Maris, 2020 lokacin da ya je karɓo kuɗin hayar gidan wani maigidan sa a Sabon Garin Zariya.
Da farko ɓarayin sun buƙaci sai an biya naira miliyan N10 za su sako shi, daga baya su ka rage kuɗin zuwa miliyan 5, sannan kuma sai aka samu matsaya da su cewa rabin miliyan za a biya.
A shekaranjiya Lahadi ɓarayin su ka buga wa iyalin waya, su ka ce ranar Talata ce ƙarshe, ko a biya su kuɗin ko su kashe shi.
A jiya ɗan sa mai suna Abba ya kai masu kuɗin, waɗanda aka tara ta hanyar karo-karo.
Wasu daga cikin marubuta da kuma wasu membobin haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu shirya finafinai ta ƙasa, MOPPAN, su na daga cikin waɗanda su ka bada gudunmawar kuɗin diyyar.
Marubutan sun haɗa da Aunty Sadiya Kaduna, Fatima Ɗanbarno, Ibrahim Sheme, da sauran su.
Masu shirya finafinai kuma sun haɗa da shugaban MOPPAN na ƙasa, Dakta Ahmad Sarari da sakataren ƙungiyar, Al-Amin Ciroma, da shugabar ƙungiyar a reshen Jihar Kaduna, Hajiya Fatima Lamaj.