FITACCEN marubucin wasan kwaikwayo kuma ɗan jarida Alhaji Yusuf Muhammad Ladan (Ɗan’iyan Zazzau kuma tsohon Hakimin Kabalan Doki cikin garin Kaduna), ya rasu a yau Talata, 10 ga Nuwamba, 2020, ya na da shekara 86 a duniya.
Ya rasu da misalin ƙarfe 8:00 na safe a gidan sa da ke Titin Maduguri, cikin garin Kaduna, bayan ya sha fama da rashin lafiya.
An yi masa sallah da misalin ƙarfe 1:00 na rana bayan sallar Azahar a babban masallacin Maiduguri Road. An kuma kai shi makwancin sa a maƙabartar da ke Titin Ɓachama da ke Tudun Wada.

Ɗimbin mutane sun halarci jana’izar, musamman da yake an jinkirta yin ta har zuwa bayan Azahar.
Mamacin ya rasu ya bar mata uku da ‘ya’ya ashirin. A cikin su akwai fitaccen ɗan jaridar nan kuma jarumin fim, Malam Abubakar Yusuf Ladan, wanda ma’aikaci ne a gidan Rediyon Tarayya na Kaduna.
A wajen zaman makokin mamacin, mujallar Fim ta tambayi Abubakar abin da zai ce game da wannan babban rashi. Sai ya amsa da cewa: “Babban rashi sai dai mu ce Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un! Duk wanda ya san cewa an haife shi, ya san cewa wata rana zai mutu. Kuma duk wanda ya sa wannan a zuciyar shi, na san cewa ba zai samu matsala ba a rayuwa.
“Wannan rasuwa ba abin mamaki ba ne, duk da mun san cewa akwai shaƙuwa tsakanin ɗa da uba, wannan shaƙuwar ya sa mu ke cewa abubuwan da ya faru, musamman na jinyar shi, Allah ya sa ya zama kaffara a gare shi.

“Sannan mutum da ya yi shekara tamanin da shida a rayuwa, tabbaci haƙiƙa sai mu gode wa Allah a wani jamin, a wani jamin kuma za ka yi baƙin ciki saboda shaƙuwa da cewa mahaifin ka ne dole za ka ji babu daɗi.
“Wannan rasuwa in na ce maka ban ji ba, gaskiya ban faɗi gaskiya ba. Na san cewa wannan rasuwa ta taɓa ni, ba wai ina jin ta kaɗan ba ne, ina jin ta sosai ne a jiki na, musamman yadda aka faɗa min labarin rasuwar, aka kira ni aka ce min ga abin da ya faru. Don haka wannan abu ba zan taɓa mantawa da shi ba.”
Da wakilin mu ya tambaye shi ko menene abin da ba zai taɓa mantawa da shi ba game da Ɗan’iya, sai Abubakar ya ce: “Abin da zan rinƙa tunawa da shi, wanda ba zan taɓa mantawa da shi a rayuwa ta ba shi ne na bi salon aikin sa. Domin aikin rediyo na shiga kamar yadda ya yi.
“Waɗannan abubuwa da ya ke yi na aikin rediyo, waɗansu na tsinci kai na a cikin su, don haka duk lokacin da na yi wani abu na kuskure ko da a rediyon ne ko ba a rediyon ba, idan ya ji ko na faɗa masa sai ya yi min gyara ya ce wuri kaza ba daidai ba ne. Kai, hatta wasu kalamai na Hausa da za ka ga wasu lokuta na kan faɗe su ba daidai ba, idan na je na same shi sai ya ce min haka ake faɗa, wancan ba daidai ba ne.
“To, irin salon aikin sa da na ɗauka shi zan rinƙa tunawa, saboda ya jiɓanci aiki na ne.
“Kuma wasu abubuwa ne da yawa da za su zo ka rinƙa tunanin wasu irin abubuwa za ka yi na rayuwa, wasu irin abubuwa ne za ka yi na cigaba ko da a rediyo ne, don shi ma’abocin sauraren rediyo ne, tunda ya daɗe ya na aikin rediyon.
“Kuma ko da sauraren rediyo ya ke yi ya ji an yi kuskure sai ya kira ni ya ce me ya sa ba a yi kaza ba? Wuri kaza ya kamata a ce an sa kaza ne.
“Duk waɗannan abubuwan su ne ba zan taɓa mantawa da su ba, tare da tarbiyyar da ya ba mu na cewa mu san na gaba da mu, sannan mu san na ƙasa da mu.”
Shi dai Alhaji Yusufu Laɗan, haifaffen Zariya ne kuma ɗa ne ga Alhaji Muhammadu Ladan, konturola na farko na gidan rediyon NBC. An haife shi a cikin 1935.
A wata hira da ya taɓa yi da mujallar Fim a cikin 2015, Alhaji Yusuf Ladan ya bayyana cewa ya fara aiki ne a Ma’aikatar Ilimi ta Lardin Arewa kafin ya koma Hukumar Rediyo ta Arewacin Nijeriya (BCNN) a Kaduna a cikin 1962.
Ya bada gagarunar gudunmawa ga cigaban aikin rediyo a Nijeriya. Ya fara aiki ne a matsayin ma’aikacin laburare, wato ɗakin aje fayafaye. Daga bisani ya koma ɓangaren shirye-shirye inda ya nuna ƙwazo ƙwarai.

Shi ne ya assasa shirye-shirye masu farin jini da su ka haɗa da ‘Yara Manyan Gobe’, ‘Basafce’, ‘Gundumi Fasa Kwanya’ (kan wasan dambe), da ‘Zaman Duniya Iyawa Ne’, kuma ya yi hirarraki da mawaƙa irin su Mamman Shata.
A hirar sa da mujallar Fim, Alhaji Yusuf Ladan ya bada labarin yadda ya rubuta waƙar Hausa ta farko da aka yi wa kiɗa a situdiyoyi aka rera ta bayan an jima ana atisayen ta; wannan ko ita ce ‘waƙar Azizu Ɗan Makaranta’ wadda Hajiya Uwani Zakirai ta rera.
Bayan haka, an wallafa wasannin kwaikwayo guda uku na Alhaji Yusuf Ladan a littafi mai suna ‘Zaman Duniya Iyawa Ne’.
Aikin gwamnati na ƙarshe da Alhaji Yusufu Ladan ya yi shi ne da ya zama Janar Manaja na gidan Rediyon Jihar Kaduna a 1987, inda daga nan ne ya yi ritaya a cikin 1991.
Shekara ɗaya kafin ya yi ritaya, sai aminin sa, Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris (wanda ya rasu kwanan baya), ya naɗa shi Ɗan’iyan Zazzau, sannan a 2001 kuma ya naɗa shi Hakimin Kabala. Amma da gwamnatin El-Rufa’i ta zo sai ta rage masarautu, wanda hakan ya shafi masarautar sa.

Daga nan ya ci gaba da zaman sa cikin hutu har zuwa lokacin da ciwon ajali ya riske shi, ya shafe watanni ya na fama. Allah ya jiƙan Alhaji Yusufu Ladan, ya sa mutuwar sa hutu ce, amin.