MARUBUTA a Kano sun ta bayyana kafa wata gidauniya ta musamman don tallafa wa iyaye da iyalan marigayi Alhaji Auwal Garba Ɗanborno.
A sanarwar da su ka bayyana a soshiyal midiya a yau Alhamis, 29 ga Yuni, 2023, marubutan, ƙarƙashin jagorancin Hajiya Umma Sulaiman ‘Yan’awaki (Aunty Baby), sun ce, “A madadin ‘yan’uwa marubuta da sauran abokan arzikin marigayi Auwal Garba Ɗanborno mu ke sanar da ku shiri na musamman domin tallafin zuri’ar ɗan’uwa, amini, musamman ta fuskar ilimin su.”
Mujallar Fim ta ruwaito labarin yadda marigayin, wanda sufeton ‘yan sanda ne kuma marubuci a Kano, ya rasu a haɗarin mota a hanyar sa ta zuwa gona a Jihar Jigawa. Ya bar matan aure biyu da iyayen sa uwa da uba da ‘ya’ya 10.
Mutuwar sa ta girgiza marubuta da sauran masoya sosai, musamman yadda ta zo ba zato ba tsammani.
Aunty Baby, wadda aminiyar marigayin ce, ta yi wani rubutu inda ta ba da sanarwar kafa gidauniyar, a ciki ta bayyana cewa babban burin Auwal Ɗanborno bai wuce ganin ya yi ƙoƙarin bai wa yaran sa tarbiyya da ilimi ba.
Ta ƙara da cewa, “Mafi girman ƙauna da karamci da masoyi zai samu daga masoyin sa bai wuce tallafar bayan sa a lokacin da ya yi ƙaura zuwa gidan gaskiya ba.
“Burin mu idan Allah ya sa mun iya haɗa abin da mu ke fata, to za mu yi ƙoƙari wurin ganin mun samar da wani abu da zai rinƙa samar da ‘yan kuɗaɗe da za mu rinƙa yin amfani da su wurin ɗawainiyar karatun yaran marigayin. Aiwatar da haka zai zama wata hanya ta tabbatar da zumunci da girmama juna tsakanin mu da iyalan marigayin masoyin mu.”
Ta bayar da asusun banki guda biyu inda duk mai sha’awar agazawa zai saka kuɗi kamar haka:
1. Rahma Abdulmajid Sharif, 2080944326, UBA
2. Umma Suleiman, 3018191777, First Bank
Aunty Baby ta ce: “Za mu riƙa saka abin da ya wakana duk wanda ya tura tallafi domin samun natsuwa da kuma sanar da halin da ake ciki.
“Allah Ubangiji ya ba mu ikon sauke wannan nauyi, ya kuma jiƙan marigayi Alh. Auwal G. Ɗanborno, ya sa shi cikin aljannar Firdausi maɗaukakiya.”
Wakilin mu ya ruwaito cewa mutane da dama sun goyi bayan kafa wannan gidauniya kuma jim kaɗan da bayyana ta har wasu sun fara turawa da tasu gudunmawar.