MASANA a Kano sun yi kira ga matasan Arewa da su tashi tsaye wajen neman ilimin harshen Turanci domin cin moriyar rayuwar zamani.
Sun faɗi haka ne a wajen taron gabatar da wani littafi mai suna “The 1000 Words Via Freedom Radio,” wanda marubuci kuma furodusan finafinai Malam Kabiru Musa Jammaje ya wallafa.
An yi taron a ranar Litinin, 30 ga Disamba, 2019 a Gidan Mambayya da ke unguwar Gwammaja a cikin birnin Kano.
Taron, wanda shi ne irin sa na farko da shahararren marubucin na Turanci ya shirya, ya yi cikar ƙwari har ta kai babu wajen zama.
Tun da farko, babban baƙo mai jawabi, Farfesa Munzali Jibril, ya bayyana muhimmancin ilimi a rayuwar matasa, musamman ma a wannan lokaci da duniya ta zamo a waje guda.
Ya ce wajibi ne matasa su nemi ilimi domin tafiyar da rayuwar su bisa tsarin da zamani ya ke tafiya a kai yanzu.
Fargesan, wanda malami ne a Jami’ar Bayero, Kano, ya ƙara da cewa, “Koyon yare a yanzu kamar Turanci abu ne da ya zama dole a rayuwa saboda yadda ya mamaye komai na rayuwa. Don haka idan za ka koyi Turanci, to abu mai muhimmancin shi ne sanin yadda za ka furta shi…
“Don haka a nan ya zama wajibi a yaba wa Kabiru Musa Jammaje saboda ƙoƙarin da ya ke yi ta hanyoyi da dama domin samar wa matasa ingantacciyar hanyar koyon Turanci a cikin yanayi mai sauƙi.”
Shi ma da ya ke jawabi, tsohon shugaban Hukumar A Daidaita Sahu ta Jihar Kano kuma malami a Jami’ar Bayero, Dakta Bala Muhammad, ya nuna takaicin sa dangane da halin da ilimi ya shiga a yau, ya na mai kira ga gwamnati da cewa abin da ya kamata ta yi a yanzu shi ne “a daidaita sahun ilimi, ba wai a daidaita sahun mashin ba.”
Shi kuma a nasa tsokacin, shugaban Buɗaɗɗiyar Jami’ar Nijeriya (NOUN), Farfesa Abdalla Uba Adamu, ya yaba da ƙoƙarin da Jammaje ya yi na samar da wannan littafi, ya na mai cewa samar da littafin ya zo a daidai lokacin da ake buƙatar sa.
Wasu malaman da fitattun mutanen da dama su ma sun yi muhimman bayanai a wajen, yayin da daga ƙarshe aka bada littafin ga mutanen da su ka halarci taron.
A jawabin sa bayan an kammala taron, Jammaje ya yi godiya ta musamman ga mahalarta taron tun daga kan malamai da su ka yi jawabai har zuwa sauran mahalarta, da kuma waɗanda su ka bada gudunmawa domin ganin an gudanar da taron.
Daga ƙarshe, ya yi fatan Allah ya kai kowa gidan sa lafiya.
