BURIN fitaccen jarumi kuma mawaƙi Garzali Mika’ilu Mailemu, wanda aka fi sani da Garzali Miko, da sahibar sa Habiba Ahmad Dikwa (Yarinya) ya cika, domin kuwa an ɗaura auren su a yau Juma’a, 20 ga Agusta, 2021.
An ɗaura auren da misalin ƙarfe 1:50 na rana a masallacin Juma’a na Alfajrul Islam da ke Maƙarfi Road, unguwar Rigasa, Kaduna a kan sadaki N200,000.
Ɗauren ya samu halartar jarumai, mawaƙa, daraktoci, furodusoshi da sauran su.
Sun haɗa da Ali Nuhu, Adam A. Zango, Lawal Ahmad, Umar M. Shareef, Umar MB, Sanusi Oscar 442, Naziru Ɗanhajiya, Auta Waziri, Saifullahi Safzor, Ibrahim Saminaka, Ubale Kd 2-Effects, ‘yan ƙungiyar Kwankwasiyya, da sauran su.

Kafin ranar ɗaurin auren an yi shagulgula a Kano, sannan gobe Asabar za a yi wani shagalin a Kano.
Haƙiƙa, a yau a wurin ɗaurin auren Garzali ya ƙara tabbar wa da duniya cewa ƙalilan daga cikin jama’a ke zagin ‘yan fim da nuna ƙin jini gare su, domin kuwa tun da aka idar da sallah jama’a su ka yi cincirindo don ganin jarumai da mawaƙan Kannywood irin su Adam A. Zango.
Ali Nuhu na cikin masallaci a wurin ɗaurin tare da su Lawal Ahmad da Umar M. Shareef, su ma an zagaye su sai ɗaukar su hoto ake yi.
Duk ba a nan ƙurar ta ke ba. Bayan an gama ɗaura aure da ƙyar da jiɓin goshi aka samu Ali Nuhu ya fita daga masallacin, domin kowa na so ya ɗauki hoto da shi ko kuma su musabaha da shi.
Haka kuma bayan ya shiga mota, sai da aka watso kuɗi daga cikin motar sannan aka samu motar ta bar harabar masallacin.

Haka shi ma Adam A. Zango, da ƙyar su ka samu su ka fita.
Abin ba a nan ya tsaya ba, domin har da mata sun fito daga gidaje don kawai su ga ‘yan fim.
Wakilin mujallar Fim ya ji wata ta na faɗin, “Da na san ‘yan fim za su zo masallacin nan da ni ma na je sallah yau!”
A kullum ana samun mutanen da ke zagin ‘yan fim da cin mutuncin su, amma kuma idan aka gan su ba a iya wucewa ba a tsaya kallon su ba.
Mu na fatan Allah ya ba Garzali da Habiba zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba.




