TSOHUWAR jaruma a masana’antar finafinai ta Kannywood, Hajiya Zakiyya Ibrahim, ta ƙalubalanci masu cewa ‘yan fim mata ba su son zaman aure da cewa ba gaskiya ba ne.
Ta yi nuni da cewa, “‘Yan fim da su ka yi aure su ka zauna sun fi waɗanda su ka yi su ka fito yawa.”
A wata da ta yi da mujallar Fim, Zakiyya ta ce: “Kawai dai su don su na gidan mijin su su na zaman aure shi ya sa ba a san su ba sai mu da mu ka fito.
“Mutane ba sa ganin abin da mu ka yi na alheri su yaba mana, shi ya sa kullum sai dai ka ji an ce ‘yan fim ba sa zaman aure.
“Amma ina da yaƙini matan da su ka yi aure ‘yan fim su ka zauna sun fi waɗanda su ka yi aure su ka fito, su na gidajen auren su, wasu ma har da ‘ya’yan su da jikoki.”
Da ta ke magana a kan mutuwar nata auren, jarumar ta ce, “Ni na yi aure ina cikin harkar fim, kuma shekara ta huɗu mu na tare da miji na, daga baya Allah ya kawo rabuwar mu.

“Amma ban taɓa tunanin na yi aure don na fito ba, sai dai da yake Allah ya ƙaddara hakan duk da miji na ya na so na ina son sa babu yadda za mu yi mu ka rabu da juna don zama na da shi babu wata matsala. Ni babbar matsalar da na samu ita ce rabuwar mu da miji na don shi rabuwar aure ba shi da daɗi, ko ba ka jin daɗin zaman gidan mijin idan aka ce auren ya mutu sai ka ji babu daɗi.”
Jarumar, wadda tuni ta dawo harkar fim ana damawa da ita, ta yi kira ga mata, musamman ‘yan fim, da su riƙe rabuwar aure da muhimmanci “domin babu abin da ya fi aure a wajen ‘ya mace.”
Ta ce, “Idan kuma ƙaddara ta sa auren ya mutu, sai mu yi haƙuri don ba haka mu ka so ba.”