MATAN da su ka yi harkar fim amma su ka yi aure kuma su ke zaune a gidajen mazan su sun kafa wata sabuwar ƙungiya domin haɗa kai da taimakon juna a tsakanin su.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa ƙungiyar, mai suna ‘Kannywood Housewives Association’ (KAHOWA), ta ƙunshi tsofaffin ‘yan fim mata da su ka yi aure sama da shekaru ashirin da waɗanda su ka yi a ‘yan shekarun nan.
Sai dai kuma wannan ƙungiya ta masu aure ce zalla, ban da zawarawa kamar yadda sauran ƙungiyoyin da aka samar a baya.
Fitattun matan da su ka kafa ƙungiyar su ne Aishar ‘Ki Yarda Da Ni’, Halima Adamu Yahaya (‘Kara Da Kiyashi’), Bilkisu Jibril, Sakna Gadaz Abdullahi, Zahra’u Shata, Fati Sulaiman, da Maijidda Abdulƙadir.
Da ta ke yi wa mujallar Fim bayani dangane da kafa ƙungiyar, Sakna Gadaz Abdullahi, wadda ta na daga cikin jagororin ƙungiyar, ta ce: “Manufar kafa wannan ƙungiyar dai shi ne domin ƙulla zumunci da kyautata alaƙar juna a tsakanin mu ‘yan fim da mu ka yi aure kuma mu ke zaune a gidan aure tare da mazajen mu, da ‘ya’ya, wasu daga cikin mu ma har da jikoki.
“Sannan wannan ƙungiyar ta KAHOWA za mu yi amfani da ita wajen faɗakar da juna muhimmancin zaman aure, sannan mu rinƙa wayar da kan mata ‘yan fim da ba su yi aure ba alherin da ke cikin zaman aure da kula da iyali, wanda mu da mu ka yi aure mu ke zaune tare da mazajen mu da yaran mu mu ke ganin hakan.

“Sannan mu na so mu kore ɗabi’ar nan ta kallon da ake yi wa ‘yan fim na cewar ba sa zaman aure, don wannan ƙungiyar ma amsa ce. Wasu daga cikin mu har ma an manta da sun yi fim saboda tun da su ka yi aure su na zaune a gidan auren su, don haka maganar ‘yan fim ba sa zaman aure wannan ba gaskiya ba ne.”
Tsohuwar jarumar ta ci gaba da cewa, “A wannan ƙungiyar za mu yi amfani da ɗan abin da ya ke hannun mu da kuma lokacin mu wajen koyar da mata sana’o’in hannu domin dogaro da kai a gidan auren su. Don haka za mu duba a cikin mu waɗanda su ke buƙatar taimako ta hanyar koya musu sana’a, ko wani kasuwanci, sai mu ga ta yadda yadda mu taimaka musu.
“Kuma alhamdu lillah a yanzu mu na matakin haɗa kan mata ne don ganin ƙungiyar ta samu gindin zama.”
Sakna ta ce nan gaba kaɗan za su shirya wani babban taro a junan su don tattaunawa a game da yadda za su tafiyar da ƙungiyar, don gudanar da ayyukan ta cikin sauƙi.
Ta ce, “Saboda haka wannan ƙungiyar mu na da manufa mai kyau ta kawo cigaba da kuma kyautata zumunci a tsakanin ‘yan fim da su ke zaune a gidan aure.”
Ta yi fatan duk abin da su ka gaza idan su ka nemi gudunmawar jama’a za su kawo masu tallafi. “Amma dai ba wai mu na roƙo ba ne ko mun kafa ƙungiyar don neman kuɗi. A matsayin mu na mata a wasu abubuwan dole idan mun gaza za mu nemi tallafi,” inji ta.