• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Matsayin mata a rubutun ƙirƙira: Hira da zakarun gasar ‘Hikaya Ta’ na shekarar 2021

by DAGA IBRAHIM SHEME
November 27, 2021
in Marubuta
0
Daga hagu: Zulaihat Alhassan, Aishatu Musa Dalil da Nana Aicha Hamissou Abdoulaye jim kaɗan bayan tattanawa da su a ofishin BBC a Abuja (Hoto daga: Ibrahim Sheme)

Daga hagu: Zulaihat Alhassan, Aishatu Musa Dalil da Nana Aicha Hamissou Abdoulaye jim kaɗan bayan tattanawa da su a ofishin BBC a Abuja (Hoto daga: Ibrahim Sheme)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A DAREN jiya a Abuja ne gidan rediyon BBC Hausa ya yi bikin karrama gwarzayen gasar rubutun gajerun labarai ta mata da ake kira ‘Hikaya Ta’. Kamar yadda mu ka ba ku labari, bikin ya yi armashi, kuma an karrama zakaru uku da su ka kai matakin ƙarshe na gasar. 

Wadda ta zo ta ɗaya a gasar ita ce Aishatu Musa Dalil, ta biyu kuma Aicha Hamissou Abdoulaye, sai ta uku Zulaihat Alhassan. 

To, a safiyar jiya ɗin, awanni kafin a tafi wajen bikin, wanda aka yi a otal ɗin Sheraton (wato tun ma kafin a san wadda ta lashe gasar), na tattauna da marubutan uku a cikin ofishin BBC Hausa da ke Abuja. Na sadu da zakarun ne a bisa gayyatar BBC ɗin, inda na zanta da su kan yadda aka yi su ka shiga gasar, da tunanin su game da matsayin mata a rubutun ƙirƙira, da fatan su game da rayuwar su bayan wannan mataki da su ka kai, da kuma tarihin rayuwar su.

Mun yi tattaunawar ne a bisa tsarin lokaci guda, ba daban-daban ba, kamar haka:

SHEME: Da farko, zan so in san sunayen ku ɗaya bayan ɗaya. Bari mu fara da ke.

AISHATU MUSA DALIL: Suna na Aishatu Musa Dalil.

SHEME: Daga wane gari ki ka zo?

DALIL: Daga Kaduna.

SHEME: Ke fa?

AICHA HAMISSOU ABDOULAYE: Nana Aicha Hamissou Abdoulaye.

SHEME: Daga ina?

AICHA: Daga Nijar na tsallako na zo Nijeriya.

SHEME: Daga Nijar ki ka shiga gasar?

AICHA: E.

SHEME: Ke fa?

ZULAIHAT ALHASSAN: Suna na Zulaihat Alhassan.

SHEME: Daga ina?

ZULAIHAT: Kaduna.

Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Badaru Abubakar Ɓaɓura, ya na miƙa kyautar karramawa ga Aishatu Musa Dalil wadda ta lashe gasar Hikaya Ta ta shekarar 2021

SHEME: ‘Yan Kaduna guda biyu su su ka ci wannan gasa kenan. To, ina taya ku murna. Allah ya sa alheri. Aisha, bari in fara da yi maki tambaya. Ya aka yi ki ka san akwai wannan gasar?

DALIL: Na farko yadda aka yi na sani shi ne, ina ƙungiyar marubuta. Akwai guruf ɗin mu inda duk marubuta su ke ciki.

SHEME: Wace ƙungiya ce?

DALIL: Ƙungiyar Marubuta kawai.

SHEME: Guruf ne a WhatsApp ko ina?

DALIL: Akwai a WhatsApp, akwai a Facebook, akwai a Twitter. Kuma mu na da website.

SHEME: Ƙungiya ce wadda ku ke haɗuwa ku yi taro?

DALIL: E, a kan haɗu a yi mitin a Skype. Sai dai a Kano su ke. To a nan ne ‘admin’ ɗin ya tura (labarin) gasar Hikaya Ta wadda BBC su ka rubuta. To da su ka tura sai su ka ce kowa zai iya shiga gasar. Sai su ka ce kowa ya rubuta ya tura masu. Da na gani, a rai na sai na ce zan rubuta, amma sai wani ran ya ce kar in rubuta! Sai na ke tambayar ɗaya rai na: “me ya sa ba zan rubuta ba?” Sai ya ce ƙungiyar da aka tura mawa manyan marubuta ne a ciki. Sai na ce ba zan rubuta ba. Amma sai na je na nuna ma maman mu, na ce mata ga shi. Ta ce in shiga in rubuta. Na ce mata, “Manyan marubuta ke shiga.” Ta ce ni ma babbar marubuciya ce, in je in rubuta! Sai na rubuta. Da na rubuta, sai na kawo mata ta karanta. Da ta karanta, sai ta ce, “Nana, ki tura!”

Sai ban tura ba duk da haka. Sai na tura ma yaya ta. Da ta karanta ita ma, ta ce in tura, ya yi labarin. Sai na ce to shi kenan.

Sai na samu marubuta da su ka san adabin Hausa sosai, da daidaitacciyar Hausa, baƙaƙen Hausa da sauran su. Sai na same su na ce su karanta min su duba min inda dakwai gyara a gyara. To alhamdu lillah, kowa ya ba ni, an duba min ƙa’idojin rubutu da abubuwa da yawa. 

To, ana gobe za a kulle (shiga) gasar Hikaya Ta na shiga. Duk da ma a ranar ban shiga ba saboda da na duba lokaci sai na ga an rubuta ƙarfe kaza an rufe amsar gasa. Sai na je sai na yi ma ‘admin’ na Marubuta magana, na ce, “Wallahi an kulle, ga shi ban shiga ba!” Sai ya ce, “Ai sun ƙara kwana biyu.” Sai na ji daɗi, sai na tura. Shi ne yadda aka yi na shiga kenan.

Uwargidan Gwamnan Jihar Kano, Dakta Hafsat Ganduje, ta na miƙa kyautar karramawa ga Nana Aicha Hamissou Abdoulaye wadda ta zo ta biyu a gasar Hikaya Ta ta shekarar 2021

SHEME: To, ɗaya Aichar, ke kuma yaya aka yi ki ka san da wannan gasar har ki ka shiga?

AICHA: To, ni bara ne na san da zaman ta. Wani marubuci ko da ya ga an fitar da ita sai ya turo mani, ya ce mani ga gasa nan in shiga. Na ce mashi, “To, in-sha Allahu zan shiga.” Bara na shiga, kuma bana ma na shiga.

SHEME: A wane gari ki ke a Nijar?

AICHA: Ina Maraɗi.

SHEME: Bakatsiniya ce kenan?

AICHA: A’a, ni ba ‘yar asalin Maraɗi ba ce, Ba’adara ce ni; ‘yar Tawa ce. Ai Maraɗi Katsinawa da Gobirawa ne.

SHEME: To Hajiya Zulaihat, ke kuma ya aka yi ki ka san da wannan gasa har ki ka shiga?

ZULAIHAT: A gaskiya ni ma’abociyar bibiyar shafukan sada zumunta ce, musamman Facebook. A nan na ke yawan bibiyar BBC Hausa. To, ina yawan ganin su na yin gasar, sai in kalla in ga yadda su ke gudanar da bukukuwan ya na burge ni. To, ‘last year’ sai na shiga, na tura labari na, ban ji wani saƙo daga gare su ba. Wannan shekarar ma ban yi ƙasa a gwiwa ba, sai na ƙara maimaita wannan labarin dai, na tura masu. Sai su ka aiko min da saƙon na yi nasara.

SHEME: Nana Aisha, ke da ma can marubuciya ce ko wannan ne karo na farko da ki ka yi rubutu?

DALIL: Ina rubutu sosai a soshiyal midiya. Labaran da na rubuta guda biyar ne.

SHEME: Labaran masu tsawo ne ko gajerun labarai ne kamar wannan na Hikaya Ta?

DALIL: A’a, masu tsawo ne gaskiya.

SHEME: Tsawon zai kai tsawon littafi?

DALIL: E, to, zan iya cewa idan zan wallafa su zan iya samun littafi na 1 da na 2 da na 3.

SHEME: Amma ba ki taɓa buga littafi ba?

DALIL: Gaskiya ban taɓa ba.

SHEME: Aichar Maraɗi – haka zan kira ki – ke da ma marubuciya ce?

AICHA: E, marubuciyar ‘online’ ce. 

SHEME: Amma ba ki taɓa yin littafi da aka buga ya fito ba?

AICHA: E. Duka a ‘online’ na rubuta. Dogon labari biyar, gajeren labari goma sha uku.

SHEME: Kin kai shekara nawa ki na rubutu?

AICHA: Shekara biyu da watanni. Watan azumi na shekarar 2019.

SHEME: Da Hausa ki ke rubutawa?

AICHA: Mn.

SHEME: Ki na da wani yare ban da Hausa?

AICHA: Ni Bahaushiya ce da man; sai Faransanci, da yake mu Faransa ne a can.

SHEME: Hajiya Zulaihat, ke da man marubuciya ce?

ZULAIHAT: E, to, ina rubutu, amma ba na (cikin) ‘online writers’. Sai dai in yi rubutu tun can shekaru da yawa, in ba ƙawaye na su karanta, su dawo min da shi in ajiye. Tun maman mu na hana ni, ina ɓoyewa. To da kuma wannan gasar ta fito sai na ce bari in kwatanta, in rubuta in tura in gani, saboda a gaskiya ni da na fi sha’awar rubutu na littafi irin na su Fauziyya D. Sulaiman – a je a buga a karanta. Da aka dawo ‘online writers’ ɗin nan ne, ban cika sha’awar rubutu a ‘online’ ba gaskiya, sai kawai na ɗan ja baya.

SHEME: Nana Aisha, bari in dawo wajen ki. Akwai wasu marubuta waɗanda da ma ki na karanta rubuce-rubucen su wanda har ya ba ki sha’awar ke ma ki zama marubuciya?

DALIL: E, gaskiya, kamar Jamila Umar Tanko da Fauziyya D. Sulasiman, zan ce su ne ‘mentors’ ɗi na. Na fi karanta littafin su, gaskiya. 

SHEME: To marubuta irin na da fa, na zamanin can baya, kamar a ce na littattafai irin su ‘Magana Jari Ce’, su ‘Ganɗoki’ da sauran su?

DALIL: E, ka san waɗannan dole a karanta su saboda a makaranta ana ɗan sa su a ‘subjects’ da ake karantawa a Hausa; sai a ba ku littafin ‘Ruwan Bagaja’, ‘Magana Jari Ce’, da dai sauran su. Iyayen mu su kan karanta mana ‘Magana Jari Ce’ da ‘Ruwan Bagaja’ tun mu na yara. Ban dai karanta su ba, amma na san su a labari.

SHEME: Aichatou, ke fa, ki na da wasu marubuta da ki ke karatun su waɗanda su ka sa ke ma ki ka ji ki na so ki zama marubuciya?

AICHA: To, kamar dai garin mu mu can akwai masu karatun su, amma ni ban karantawa sai ina sauraren wanda ake yi a gidan rediyo. Ina sauraren na Sumayya Abdulƙadir, da Fatima Husseini El-Ladan da su Fauziyya D. Sulaiman; ina sauraren littattafan su. Amma dai irin waɗannan ban taɓa karantawa ba. Amma dai ‘online’ gaskiya akwai waɗanda su ke burge ni, ina son labaran su, kamar su Rufaida Umar wadda ta zo ta uku a gasar bara. Gaskiya ta iya labari, ta na burge ni!

SHEME: Zulaihat, kin ambaci Fauziyya D. Sulaiman ɗazu. Ko akwai waɗansu littattafan waɗanda su ka sa ki ki ka samu shauƙin yin rubutu?

ZULAIHAT: Akwai su, gaskiya.

SHEME: Kamar su wa?

ZULAIHAT: Akwai Anti Bilkisu Funtuwa, akwai Jamila Umar Tanko, akwai Sumayya Abdulƙadir, Zainab, Sa’adatu Waziri Gombe, Maryam Mashi, su na dawa gaskiya, don na yi karatu sosai.

SHEME: Aisha, yaya sunan labarin da ki ka rubuta na shiga wannan gasa ta Hikaya Ta?

DALIL: Sunan labarin ‘Haƙƙi Na’.

SHEME: Labarin menene?

DALIL: Fyaɗe.

SHEME: To yaya ki ka ji da aka sanar da ke cewa ki na daga cikin waɗanda su ka yi nasara?

DALIL: Ina bacci aka sanar min! Ina barci waya na ta yi ɗara, na ɗauka, Fauziyya (ta BBC Hausa) ta ce min ina daga cikin waɗanda labarai guda uku da su ka ci gasar nan. Kawai sai na miƙe na yi sujudul shukur; ba ma hijabi a jiki na. Murnar ta yi min yawa ma, kawai na faɗi na yi wa Allah godiya saboda na san Shi ya ba ni wannan nasarar.

SHEME: Ke fa Aicha? Wane labari ki ka rubuta?

AICHA: Labarin ‘Butulci’.

 SHEME: A kan menene?

AICHA: Butulci ne miji ya yi ma matar shi saboda mahaifin ta ya na da kuɗi hakan ga sosai, kamar ma dai da ma ya arme ta da farko, kawai don ya kashe mahaifin ta ne, idan ya kashe mahaifin ta zai samu dukiyar mahaifin nata, daga nan kawai sai ya sallame ta. To bai samu kawar da ita ɗin ba, sai ya yi garkuwa da matar tashi. 

SHEME: To ya ki ka ji da aka kira ki aka ce maki ki na daga cikin waɗanda su ka yi nasara, kuma ki na ina a lokacin?

AICHA: Ina kwance ban da lafiya, na ga kira daga Nijeriya, na ce, “To, wa ke kira na wajen ƙarfe 9 na dare daga Nijeriya?” To da yake ina hulɗa sosai da ‘yan Nijeriya marubuta, kawai sai na ɗaga. Ina ɗagawa, sai bayan ta yi min sallama ta ce sunan ta Fauziyya daga BBC. Sai na tashi daga kwance a na ke, na rungume ƙanwa ta ta na zaune ta na sa caji, da na ji ta  ce, “Ina farin cikin sanar da ke cewa labarin ki…” sai na ce, “Allahu Akbar! Allahu Akbar! Alhamdu lillah!” Sai ina ta kuka, hawaye su na ta zubo min saboda murna.

SHEME: Zulaihat fa, yaya sunan labarin ki?

ZULAIHAT: “Rahmat”.

SHEME: A kan menene?

ZULAIHAT: A kan adalci da gaskiya da kuma fyaɗe.

SHEME: To yaya aka yi aka kira ki aka sanar da ke kin yi nasara?

ZULAIHAT: To, da (Fauziyya Tukur) ta kira ni da daddare dai gaskiya na yi bacci, saboda ina saurin bacci. Da safe, na ga ‘missed call’ amma ban san wa ke da namban ba. To akwai aminiya ta da ta ke yawan sauraren BBC ko da yaushe da safe; sai na ga ta kira ni a waya, don ta san na yi rubutun. Sai ta ce min, “Ke, labarin ki ya na cikin labaran da aka zaɓa, ‘Rahmat’.” 

Sai na ji kamar ƙarya ta ke yi – gaskiya ne, ba gaskiya ba ne? Na ce, “Kin saurara kuwa?” Ta ce, “Na saurara yau da safe.” Sai na ce, “To ni ba a kira ni ba amma na ga ‘missed call’ guda ɗaya da wata namba.” Sai ta ce, “To ki kira nambar ki ji.” Sai na kira, na kira ba a ɗauka ba. Sai na koma i-mel ɗi na da na tura saƙo, sai na duba namban, sai na ga namban Fauziyya ne. Sai na dinga tsalle tun kafin ma ta kira ni.

SHEME: Nana Aisha, yanzu wane buri ki ke da shi a matsayin ki na marubuciya? Me ki ke hangen za ki iya zama a wannan fage na rubutu tunda ga shi Allah ya sa ki na daga cikin waɗanda su ka yi nasara a wannan gasa? 

DALIL: Ina hangen cewa kila ma har rubutun finafinai zan fara a matsayi na kuma na marubuciya.

SHEME: Za ki so ki zama fitacciyar marubuciya ban da kawai ta ‘online’?

DALIL: Ina so in zama fitacciyar marubuciya har wacce ta ke ‘publishing’. Sannan ban so in tsaya kawai a rubutun Hausa, ina so in haɗa har da Ingilishi.

SHEME: Kin taɓa yin na Turancin?

DALIL: E, na taɓa.

SHEME: An buga shi ne?

DALIL: A’a, a ‘Wordpad’ ne.

SHEME: Ba ki wallafa shi ba ko da a soshiyal midiya?

DALIL: A’a, ai ‘Wordpad’ ma wani ‘website’ ne da ake karanta labarai. Shi kawai ya ƙunshi labarai, za ka je ka yi ‘posting’ a wurin.

SHEME: Ke fa ɗaya Aichar, me ki ke gani? Wannan nasarar ta za buɗe maki wasu ƙofofin ne?

AICHA: To ina fatan wannan nasara ta buɗe mani ƙofofin nasarori, su buɗe mani a rayuwa ta da ni da ‘yan’uwa na waɗanda su ke tare da ni, da ma sauran marubuta baki ɗaya.

Malam Sadiq Mai Borno, Mataimakin Manajan Darakta na kamfanin iskar gas na Nijeriya (NLNG), ya na miƙa kyautar karramawa ga Zulaihat Alhassan wadda ta zo ta uku a gasar Hikaya Ta ta shekarar 2021 … jiya a Abuja

SHEME: Zulaihat, wane ƙwarin gwiwa wannan nasara ta ba ki, kuma me ki ke son ki cimmawa daga yanzu?

ZULAIHAT: Gaskiya, ta ba ni ƙwarin gwiwa sosai don yanzu na ke jin na ƙara samun ƙarfi da ƙarin in ƙara ƙarfi wurin rubutu na, saboda ina da burin in zama babbar marubuciyar da duniya za ta yi alfahari da ita, kuma in na yi rubutu saƙon da na ke son isarwa ya isa ga al’umma da dama. 

SHEME: Wane kira ki ke da shi ga sauran matasa, musamman mata, a game da zama marubuta?

ZULAIHAT: To, kiran da na ke da shi a game da mata shi ne in su na da rubutu ko labari da su ke da shi – don wasu akwai labarin a kan su, da niyyar, amma tsoro da rashin ƙwarin gwiwa ya na hana su – su fito su yi ‘voicing’ abin da ke damun su. To kuma wani abin ne ya ke damun shi a cikin ran shi a kan abin da ya faru ga wani, wani kuma ƙagagge ne, ya na so ya bada ne duniya ta amfana da shi, amma sai ya ga kamar ba zai yi nasara ba. Su samu ƙwarin gwiwa, su daina karaya, su fitar da abin da ke cikin zukatan su ta hanyar rubutu.

SHEME: To Aishar Maraɗi, wane kira za ki yi ga matasa game da harkar rubutu, musamman mata?

AICHA: Kira na ga marubuta manya da ƴanana iri na shi ne su jajirce, su nemi sani game da abin da za su rubuta, su yi bincike; abin da ya shige masu duhu su tambayi waɗanda su ka fi su sani. Kuma su ji tsoron Allah a duk abin da za su rubuta, su san me za su riƙa rubutawa. Kuma kar su tsaya a kan jigo guda, su nemi jigo wanda in mutum ya karanta ya ji wannan labarin kamar ma allon rayuwar wani ne ya ke kallo, ya ji kamar abin ya na faruwa ne a zahiri. kun ga kenan idan mutum na irin wannan rubutun, in-sha Allahu saƙon shi zai isa ga al’ummar shi da har wata al’ummar ta duniya gaba ɗaya.

SHEME: Nana Aisha, ke wane kira za ki yi ga matasa, musamman mata tunda wannan gasa ta Hikaya Ta ta mata ce?

DALIL: Ita dai rubutu, ka na fitar da zancen da ke cikin zuciyar ka ne. Zan iya cewa yawancin mata mu na fuskantar ƙalubale, kuma wani ya na so ya rubuta amma ya na tsoro, bai so ya rubuta. Yawancin mata ‘we are the voice of the voiceless’: mu na son mu yi rubutu amma ana rasa ƙwarin gwiwa. To ina so su sa ‘determination’, su saka a ran su  za su iya. Don ba su iya abu ba, su riƙa tambayar na gaba da su. 

Su ma manyan marubuta, don Allah ina roƙon su, ƙananan marubutan nan su riƙa gina su. Za ka ga wani babban marubucin, sai ka ga wasun su  – amma ba duka ba – ba su ‘encouraging’ ƙananan; in su ka ba su gyara ba su gyarawa. Idan mun haɗa kai mun zama tsintsiya-maɗaurin-ki-ɗaya, sai ka ga rubutun ya kai duk inda ake buƙata, kuma mun isar da labari, mun isar da saƙo. Wani ba zai gan ka ido da ido ba amma ta hanyar rubutun ka, in ya karanta, wani a rubutun da ka yi ko ya canja rayuwar shi ko ya ya ji tsoron aikata wani abu, ko ya samu wani ilimi dai. Shi ne duk wata wadda ta ke da burin zama marubuciya, ta sa a ran ta za ta iya. Kuma ta riƙa bibiyar labarai sosai, ta na karantawa. Ina jin hakan zai ƙara taimaka masu wajen yunƙurin su tashi su zama marubuta. Su riƙa kuma shiga gasanni su na ‘competing’, in-sha Allahu Allah zai dafa mana gaba ɗaya.

SHEME: Ki na ganin mata marubuta rubutun su zai iya zama daban da na maza? Mata su na da wasu matsaloli na musamman ne waɗanda za su isar, waɗanda su ka bambanta da na maza? 

DALIL: Matsalolin da mu mata mu ke fuskanta ya fi na maza. Idan mu mata za mu fito mu yi magana mu rubuta, maza su fito su yi magana su rubuta, zan iya cewa za a ɗauki uku, in dai ba a bi ƙa’idojin rubutu da daidaitacciyar Hausa ba, za a iya cewa labarin ‘ya mace zai buge na namiji saboda mu na da abubuwa da yawa waɗanda mu mata mu ke fuskanta na ƙalubale. Misali, al’amurran nan na fyaɗe da dai sauran matsalolin gidajen aure, da abubuwa dai da yawa; ‘ya mace ta fi namiji shan wahalar rayuwa a wasu ɓangarorin.

SHEME: Har da abubuwan da su ka danganci kiwon lafiya, da sauran su.

DALIL: Har da abubuwan da su ka danganci kiwon lafiya.

SHEME: Da rashin tsaro…

DALIL: Da rashin tsaro, (amma) wannan za a iya cewa ya shafi maza da mata ne. Amma zan iya cewa kashi 70 cikin ɗari ya fi shafar mata, sauran kashi 30 kuma maza.

SHEME: Aicha, kin yarda da cewa matsalolin mata sun fi na maza yawa kuma ya kamata a fito da su ta hanyar rubutu?

AICHA: To, matsaloli kowa ya na da matsaloli, amma kamar mata su na shan wahala saboda su su na da rauni. Namiji ko ya na shan wahala, saboda rashin raunin shi wani ya na iya ɓoyewa haka. Amma mace rauni ya yi mata yawa, shi ya sa in ta na cikin matsala yawanci kowa sai ya sani. 

SHEME: Zulaihat, me za ki ce kan wannan maganar ta matsalolin mata a rubutu?

ZULAIHAT: Kamar yadda ‘yan’uwa na su ka faɗa, mun fi maza fuskantar matsaloli. Kuma abin da ya sa mu matsalolin mu kamar a bayyane su ke (shi ne) saboda mu ba mu da juriya; mu na da rauni. Namiji ko abu na damun shi, zai jure a matsayin shi na namiji, mace kuwa sanyayyar zuciya ne da ita; raunin ta ya yi yawa.

Kuma mu mu ka fi fuskantar matsaloli da yawa. Kamar ka ga al’amarin fyaɗe, in aka yi za a ce a yi shiru saboda martabar ta, saboda al’adun mu, kar a ɗaga maganar. Sannan in an kai abin a matakin gaba ba a yin hukunci da mace za ta samu gamsuwa; wani kafin ya kai inda za a zartar da hukuncin ma an daƙile maganar. Shi ya sa kamar a labari na, uwa ce da kan ta ta fito a matsayin ‘yar sanda da uban, kuma ɗan su shi ne guda ɗaya da su ka haifa, amma ya yi ma ‘yar aikin gidan ta fyaɗe. ‘Yar aikin tata yare ce, ba ta yi dubi da yare ko addini ba da cewa ɗan nata shi ɗaya ne, ta tsaya ta jajirce aka yi adalci, aka yanke masa hukuncin da ya kamata. 

To yawancin mata mu na fuskar irin waɗannan matsalolin, in ba a yi hukunci ba sai ka ga wannan ‘frustration’ da ke damun mu ya sa mun shiga wani yanayi na damuwa.

Kamar da ta yi magana a kan matsalolin kidinafin, in ya shafi mace, ka ga mace in aka ɗauki mijin ko aka tafi da ita, an fi fargaba a kan ta saboda za a wulaƙanta martabar ta. Shi namiji in Allah ya taimake shi, iyaka duka ne kawai zai sha; duk da shi ma ba daɗi ba ne, amma nata matsalar ya fi cin rai. 

Sannan a gidajen aure mata na fuskantar matsaloli da ba sa iya buɗe baki su faɗi. Ko sun faɗi sai a ce a yi haƙuri. Wani abin kuwa haƙuri bai yi, sai an ɗau mataki, don idan wani ya ga an ɗauki mataki to zai kiyayi abin da zai yi. Amma rashin ɗaukar matakin shi zai sa kowa ya yi abin da ya ga dama, sai a ce, “Ai ba abin da zai faru!”

SHEME: Tambayar ƙarshe, ina so ku ba ni taƙaitaccen tarihin ku. Bari in fara da ke Zulaihat.

ZULAIHAT: To, kamar yadda na faɗa, suna na Zulaihat Alhassan. Ni haifaffiyar garin Kaduna ce, a Ƙaramar Hukumar Kaduna South, cikin unguwar Maƙera Kakuri. Na yi ‘primary school’ ɗi na a ‘Nasarawa 2 LGA Primary School’, Sabon Gari. Na yi ‘secondary school’ ɗi na a GGSS Kawo, Kaduna. Sannan na wuce ‘College of Health Science and Technology’, inda na karanta ‘Dental Health Technician’.

To, bayan na gama, na yi aiki da wasu asibitoci masu zaman kan su. Sai na ƙara komawa makarantar, ina karantar fannin ‘Dental Theraphy’, yanzu ina shekarar ƙarshe. 

Na kan ɗan taɓa kasuwanci ba laifi.

SHEME: Shekarar ki nawa yanzu?

ZULAIHAT: An haife ni a ranar 3 ga watan 3, shekara ta 1992. Ka ga shekaru na 29.

SHEME: Aichar Maraɗi, ba mu tarihin ki.

AICHA: Suna na Nana Aicha Hamissou Abdoulaye daga Maraɗi, Jamhuriyar Nijar. Na yi ‘primary school’ a wata makaranta da ake ce mata ‘Ecole Sabon Gari’ a unguwar Zarya a cikin Maraɗin. Na yi sakandare a unguwar Zarya. Sannan na yi Ɗanbaskore, nan na ida sakandare ɗi na. 

Bayan na gama, na tafi Jami’ar Maraɗi ta Ɗandukko, nan na yi digiri na na farko a kan ‘Environmente’. Yanzu haka ina ‘Masters’ ɗi na a ‘Aboubacar Ibrahim International Universite’, ina karanta ‘Animal Science and Biodiversity’.

SHEME: Yanzu shekarar ki nawa?

AICHA: Ashirin da bakwai.

Zakarun gasar Hikaya Ta ta shekarar 2021 kowacce da kambin karramawar ta a wurin bikin da BBC Hausa su ka shirya a daren jiya a Abuja

SHEME: To, Nana Aisha, sauran ke.

DALIL: Suna na Aisha Musa Dalil, daga Jihar Kaduna. An haife ni kuma na girma a Kaduna. Na yi firamare da sakandire ɗi na duk a garin Kaduna. Daga nan kuma na tafi Jami’ar Umaru Musa Yar’Adua (a Katsina) inda na ke karanta fannin ‘Linguistics’, ina karanta ‘English and French’.

SHEME: Ke Bakatsiniya ce da ganin ki!

DALIL (dariya): A’a, ni ‘yar Adamawa ce.

SHEME: Shekarar ki nawa?

DALIL: Shekara ta goma sha takwas.

SHEME: Sha-takwas kacal? Ke ce ƙarama kenan a nan.

DALIL: E, haka ne.

SHEME: To, Allah ya taimaka. Na gode maku ƙwarai da wannan tattaunawa da na yi da ku.

SU DUKA: Mu ma mun gode.

Loading

Tags: Adabin HausaAicha Hamissou AbdoulayeAishatu Musa DalilBBC HausaHikaya TaKadunaMaradimarubutaZulaihat Alhassan
Previous Post

Za a bayyana gwarzuwar gasar rubutu ta ‘Hikayata’ ta 2021 a daren yau

Next Post

Hamisu Jibrin Goma ya zama sabon shugaban masu shirya fim na Kaduna

Related Posts

Gasar rubutu: Ba a taɓa ba marubutan Hausa dama irin wannan ba – Balannaji 
Marubuta

Gasar rubutu: Ba a taɓa ba marubutan Hausa dama irin wannan ba – Balannaji 

January 1, 2025
Zubairu Balannaji ya zama gwarzon gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

Zubairu Balannaji ya zama gwarzon gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai

December 31, 2024
‘Dakan ɗaka…’: Kanawa sun lashe gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

‘Dakan ɗaka…’: Kanawa sun lashe gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai

December 20, 2024
Mutane 15 sun yi nasarar zuwa zagayen kusa da na ƙarshe a gasar rubutu na Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

Mutane 15 sun yi nasarar zuwa zagayen kusa da na ƙarshe a gasar rubutu na Hukumar Tace Finafinai

November 30, 2024
Tsakanin matan aure biyu da budurwa ɗaya za a san gwarzuwar gasar Hikayata ta 2024 a yau
Marubuta

Tsakanin matan aure biyu da budurwa ɗaya za a san gwarzuwar gasar Hikayata ta 2024 a yau

November 27, 2024
Ƙungiyar matasa da mata za ta naɗa Ado Gidan Dabino Sarkin Mawallafan Arewa
Marubuta

Gasar rubutu: Hukumar Tace Finafinai ta bayyana gwaraza 50 na zagayen farko

November 24, 2024
Next Post
Dama zuwa hagu: Sha'ani, Goma, da Maina su na karɓar rantsuwa daga Barista Jamilu Sulaiman jim kaɗan bayan an zaɓe su a matsayin shugabannin MOPPAN na Jihar Kaduna

Hamisu Jibrin Goma ya zama sabon shugaban masu shirya fim na Kaduna

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!