‘YAN biyu kyautar Allah. A daren Lahadi, 3 ga Afrilu, 2023 Allah ya azurta mawaƙi a Kannywood, El-Bash Muhammad, da tagwaye, mace da namiji.
Maiɗakin sa A’isha ta haihu da misalin ƙarfe 3:30 na dare a asibitin gwamnati da ke Kawo, Kaduna. Sai dai bayan haihuwar, an tura su Asibitin Tunawa Da Yusuf Ɗantsoho da ke Tudun Wada inda a nan za a raine su cikin kwalba har na tsawon kwana uku saboda su ƙara ƙwari.

El-Bash ya shaida wa mujallar Fim cewa babu wani suna da ya raɗa masu, ya bar masu Hassana da Hussaini.
Haka kuma ya ce ba za su yi taron suna ba, sai dai walimar shan ruwa.
Allah ya raya Hassana da Hussaini, amin.