MAWAƘI a Kannywood, Alhaji Sanusi Ɗahiru Pambeguwa, ya aurar da ‘yar sa Fatima a jiya Asabar.
An ɗaurin auren Fatima Sanusi Pambeguwa da habibin ta Yusuf Sani a jiya Asabar, da misalin ƙarfe 2:00 na rana a gidan marigayi Alhaji Ɗahiru Dillalin Masara, Pambeguwa, Jihar Kaduna, a kan sadaki N300,000.
Wasu daga cikin waɗanda suka halarci ɗaurin auren sun haɗa da Alhaji Ɗahiru Mai Dusa, Alhaji Haruna O.G. Pambeguwa, Akanta Janar na Jihar Kaduna, Honarabul Bashir Sulaiman Zuntu, Shugaban Ƙaramar Hukumar Kubau, Isah Sale Banki, sai kuma ‘yan kasuwa da ‘yan siyasa.

Mawaƙin ya shaida wa mujallar Fim cewa babu mawaƙi ko ɗan fim ɗin da ya halarci ɗaurin auren, amma wasu sun kira shi sun yi masa Allah ya sanya alheri.
Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba.