YAU dai ta tabbata mawaƙi a Kannywood, Adamu Mohammed Turaki, wanda aka fi sani da A. Wamba, ya yi bankwana da kwanan situdiyo.
Kamar yadda mu ka sanar da ku, yau za a ɗaura auren sa a garin su, Wamba, da ke Jihar Nassarawa. Cikin hukuncin Allah, A. Wamba ya zama angon Hadiza Hassan Galadima (Hadiza Mamah).
An ɗaura auren su a yau Asabar, 4 ga Fabrairu, 2023, da misalin ƙarfe 11:00 na safe, a fadar mai martaba Sarki Oriye Rindre na Wamba, Jihar Nassarawa, a kan sadaki N400,000.

‘Yan Kannywood da su ka halarci ɗaurin auren sun haɗa da Lilin Baba, Umar M. Shareef, Abdul D. One, Umar Big Show, Muhammad Maileri, Shatan Sojoji, Murtala Buloko, Yasir Ahmad, Denzin Arewa da Abdul Tynking Maigashi.
An shirya ƙasataccen bikin dina na musamman don taya ango da amarya murna.
Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba.
