SHAHARARREN mawaƙin gambara (Hip-hop) a Kannywood, Malam Aminu Abba Umar, wanda aka fi sani da suna Nomiis Gee, ya samu ƙaruwar ‘ya mace.
Mai ɗakin sa, Malama Fatima Bashir Aminu, ta haihu a ranar Talata, 3 ga Satumba, 2024 da misalin ƙarfe 10:00 na safe a wani asibiti mai suna ‘International Clinic’ da ke Bata, Kano.
An raɗa wa jaririyar suna Rahama, amma za a riƙa kiran ta da Amaya.
Nomiis Gee ya shaida wa mujallar Fim cewa sunan mahaifiyar sa ya raɗa wa jaririyar.
Ya ƙara da cewa, “Ranar Talata ne suna, amma ba za a yi taron suna ba. Sai dai taron ‘yan’uwa, wato family.”
Ya kuma miƙa godiyar sa ga jama’a da ke ta zuwa yi masu barka da fatan alkhairi.
A yanzu dai ‘ya’yan Nomiis Gee biyu ne, wato Muhammad Zayn da Rahama (Amaya).
Allah ya raya su, ya albarkaci rayuwar su.
