ALLAH ya azurta mawaƙi, furodusa kuma jarumi a Kannywood, Malam Salisu Nuhu Mariri, da samun ƙaruwar ɗa namiji.
Matar sa ta haifi yaron cikin ƙoshin lafiya a ranar Talata, 4 ga Satumba, 2023 a Asibitin King’s Gate da ke yankin Hotoro GRA a cikin garin Kano.
An yi taron suna a ranar Talata da ta gabata inda aka raɗa wa jaririn suna Nuhu, wanda kuma ake yi masa laƙabi da Mu’allim.
Allah ya raya shi cikin salihan bayi, amin.