ALHAMDU LILLAHI! Allah ya yi, shi ma fitaccen mawaƙin nan mazaunin Kaduna, Umar Musa, wanda aka fi sani da Umar Ɗan-Hausa, ya yi bankwana da kwanan situdiyo.
A ranar Asabar, 30 ga Janairu, 2021 aka ɗaura masa aure da sahibar sa Fatima Bashir.
An ɗaura auren da misalin ƙarfe 1:00 na rana, bayan sallar azahar a masallacin Juma’a na Ɗanfodiyo da ke Unguwar Sanusi, Kaduna, a bisa sadaki N50,000.

Wasu daga cikin waɗanda su ka halarci ɗaurin auren sun haɗa da Kwamishinan ‘Yansanda na Jihar Kaduna, Alhaji Umar Musa Muri, da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Dakta Muktar Ramalan Yero, da Dakta Hakeem Baba Ahmed, Alhaji Tukur Abdulƙadir, Honarabul Kabiru Classic, Aminu Ladan Abubakar (ALA), Malam Yahaya Makaho, El-Mu’az Birniwa, Sagir Baban Kausar, Jibril Jalatu, da sauran su.
Bayan ɗaurin auren, an yi walima a harabar ofishin Malam Yahaya Makaho da ke Titin Constitution. Sai dai a wurin walimar, tilawar karatun Alƙur’ani mawaƙa su ka yi, ɗaya bayan ɗaya.
Allah ya ba Umar Ɗan-Hausa da amarya Fatima zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba, amin.
