FITACCEN mawaƙin Kannywood Musa Muhammad, wanda aka fi sani da suna Ɗan Musa Gombe, zai zama ango a makon gobe.
Mawaƙin ya bayyana haka ne a saƙon gayyatar ɗaurin auren da ya tura a Instagram.
Ya ce, “Salam. Ina gayyatar ‘yan’uwa da abokan arziƙi zuwa wurin ɗaurin aure na. Allah ya ba kowa ikon zuwa.”
Za a ɗaura auren Ɗan Musa Gombe da sahibar sa Salmah Abdulazeez Chado a ranar Asabar mai zuwa, 17 ga Satumba, 2022, da misalin ƙarfe 10:00 na safe a Masallacin Murtala da ke unguwar Hausawa, a birnin Kano.