FITACCEN mawaƙi a Kannywood, Aliyu Isa Nata, ya bayyana cewa duk wanda ya halarci ɗaurin auren sa ya ga ya yi kuka da idon sa don ganin yadda al’umma su ka cika.
A hirar da angon ya yi da mujallar Fim kwana biyu bayan an ɗaura auren sa da amaryar sa, Zainab Suleiman (Zee Fulani) a Katsina, ya labarta mana yadda jama’a su ka yi masa kara.
Aliyu ya ce: “Babu abin da zan ce sai dai in ce na gode wa Allah da al’umma baki ɗaya. Gaskiya na ga hidima, na ga kara, na ga kuma al’umma.
“Duk wanda ya je ɗaurin auren ya ga lokacin da har kuka na yi da ido na. Domin duk shagulgulan da na lissafa maka, babu inda bai cika da al’umma ba. Mutane na ta kira na su na cewa na gode wa Allah. Abokan sana’a ta na Katsina su na kira na su na ce mani tun da aka kafa industiri ba a taɓa bikin wani mawaƙi ko ɗan fim da aka cika haka ba.
“Babu abin da zan ce sai godiya ga Allah, don jama’a rahama ne.”

An dai ɗaura auren Aliyu da Zee Fulani a safiyar ranar Asabar, 20 ga Agusta, 2021 da misalin ƙarfe 11:30 na safe a masallacin Ƙofar Durɓi, Katsina, a kan sadaki N50,000.
Ɗaurin auren ya samu halartar jarumai, mawaƙa, daraktoci, furodusoshi da sauran su.
A cikin su akwai Abdul Amart, Sadiq M. Mafiya, Ado Isa Gwanja, Hamisu Breaker, Sadiq Sani Sadiq, Alfazazee, Isah Bawa Doro, Fresh Emir, Musty Opera da sauran su.
Wasu daga cikin ‘yan fim mata da su ka halarci bikin sun haɗa da Momee Gombe, Maryam Yahaya, Meenal Ahmad, Hadiza Ahmad, Teema Yola da sauran su.
A manyan mutane da su ka halarci ɗaurin auren akwai Alhaji Abdulazeez Maituraka da Alhaji Babangida P.A.

Kafin ranar ɗaurin auren an yi shagulgula irin su Ranar Larabawa (Arabian Night), Ranar Fulani (Fulani Day), ƙwallon ƙafa, da dina da aka yi ana gobe ɗaurin auren.
Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba.

