• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Minista na so kafafen yaɗa labarai su daina yayata ayyukan ’yan ta’adda da ’yan bindiga

by WAKILIN MU
May 7, 2025
in Nijeriya
0
Minista na so kafafen yaɗa labarai su daina yayata ayyukan ’yan ta’adda da ’yan bindiga

Alhaji Mohammed Idris yana gabatar da jawabi a taron

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga ‘yan jarida da su guji tallata ’yan ta’adda da ‘yan bindiga da sauran miyagu da ke barazana ga zaman lafiya da tsaron ƙasar nan.

Ministan ya bayyana haka ne a yau Laraba yayin zama na bakwai na Jerin Zauren Bayanai na Ministoci na shekarar 2025 wanda aka gudanar a Cibiyar Yaɗa Labarai ta Ƙasa da ke Abuja.

Idris ya ce, “Kafofin yaɗa labarai, a matsayin su na masu tantance labarai kuma abokan hulɗa wajen gina ƙasa, suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen ƙarfafa gwiwar dakarun mu ta hanyar nuna irin nasarorin da suka samu da sadaukarwar da suke yi.

“Dole ne mu guji tallata waɗannan ƙungiyoyi. Dole ne mu cire su daga shafukan farko na jaridu, mu riƙa bayar da rahoto a kan su daidai da yadda suke — wato masu laifi ne — ba tare da ƙawata ayyukan su ko ba da muhimmanci ga ƙarya da farfagandar da suke yaɗawa ba.”

Ministan ya ƙara da cewa ‘yan ta’adda da sauran miyagun ƙungiyoyi suna amfani da kafafen watsa labarai da na sada zumunta ne domin su yaɗa fargaba da ƙarya da kuma jawo mutane zuwa gare su.

Saboda haka, ya buƙaci ’yan jarida da editoci da su zama masu kishin ƙasa da ƙwarewa wajen bayar da rahoto, ta hanyar guje wa manyan kanun labarai masu tayar da hankali da kuma ƙin zama hanyar yaɗa farfaganda ta masu aikata ta’addanci.

Alhaji Mohammed Idris (a tsakiya) tare da Ministan Tsaro, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar (a dama), da Ministan Muhalli, Alhaji Balarabe Abbas, a taron

Ya ce: “Waɗannan ba ‘yan gwagwarmayar ‘yanci ba ne; masu kisa ne, masu sace mutane ne, masu ɓarna ne, kuma dole ne a bayyana su a hakan.”

Ministan ya kuma haskaka wani muhimmin ɓangare na Ajandar Sabunta Fata ta Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, musamman ɓangaren da ya shafi “Ƙarfafa Tsaron Ƙasa Don Samar Da Zaman Lafiya Da Cigaba.”

Ya ce Gwamnatin Tarayya tana ci gaba da kashe kuɗi wajen samar da kayan aiki na zamani ga sojoji, da inganta binciken leƙen asiri da kuma haɓaka haɗin gwiwa da ƙasashen duniya.

Wani sashe na mahalarta

Idris ya bayyana cewa Jerin Zauren Bayanai na Ministocin wani shiri ne da ma’aikatar sa ta ƙirƙira domin bai wa ministoci dama su faɗa wa ’yan Nijeriya irin nasarorin da suke samu, da ayyukan da ke gudana da kuma tsare-tsaren da za su aiwatar a nan gaba.

Ya ce, “Ta wannan dandali na tattaunawa, wanda ake watsawa kai-tsaye a tashoshin talbijin na ƙasa da kuma kafafen sada zumunta, muna ci gaba da nuna jajircewar mu ga gaskiya, ɗaukar nauyi, da haɗin kai da jama’a.”

Ministan ya yaba wa kafafen yaɗa labarai bisa goyon bayan da suke ba wannan shiri da kuma rawar da suke takawa wajen wayar da kan al’umma game da ayyukan gwamnati.

A taron, Ministan Tsaro, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, da Ministan Muhalli, Alhaji Balarabe Abbas, sun gabatar da bayanai ga manema labarai kan nasarorin da ma’aikatun su suke samu.

Loading

Tags: 'yan bindiga'yan ta'addakidinafasMohammed Idrisrashin tsaro
Previous Post

Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta fara bitar ayyuka na tsakiyar wa’adi

Next Post

Ƙungiyar Sadarwa ta Ƙasa ta kammala bitar ayyukan ta, ta fitar da sababbin matakan tallata nasarorin gwamnatin Tinubu

Related Posts

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Next Post
Ƙungiyar Sadarwa ta Ƙasa ta kammala bitar ayyukan ta, ta fitar da sababbin matakan tallata nasarorin gwamnatin Tinubu

Ƙungiyar Sadarwa ta Ƙasa ta kammala bitar ayyukan ta, ta fitar da sababbin matakan tallata nasarorin gwamnatin Tinubu

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!