• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 16, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Minista Sadiya ta buƙaci a kula da naƙasassu yadda ake yi a manyan ƙasashe

by DAGA WAKILIN MU
January 9, 2021
in Nijeriya
0
Minista Sadiya ta buƙaci a kula da naƙasassu yadda ake yi a manyan ƙasashe
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAR Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta samar wa da naƙasassun da ke Nijeriya hanyoyin da za su riƙa bi a dukkan gine-gine da wurare na gwamnati irin su filayen jirgin sama, tashoshin jirgin ƙasa da na mota da makarantu.


Ministar ta yi kiran ne a lokacin da ta gabatar da Shugaba da membobi da Babban Sakataren Cibiyar Naƙasassu ta Ƙasa ga Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis a fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Shugaba Buhari da Minista Sadiya Umar Farouq tare da membobin Hukumar Naƙasassu ta Ƙasa a lokacin ziyarar a fadar shugaban ƙasa
Shugaba Buhari da Hajiya Sadiya Umar Farouq


Hajiya Sadiya ta gode wa Shugaban Ƙasa saboda yadda ya amsa kiran naƙasassun ta hanyar rattaba hannu kan Dokar Kula da Naƙasassu ta Ƙasa sannan ya kafa Hukumar Naƙasassu ta Ƙasa. Amma ta yi nuni da cewa mutane masu naƙasa a ƙasar nan an ware su daga cin moriyar wasu ababe na more rayuwa. 


Ta ce sama da kashi 95 cikin ɗari na gine-ginen gwamnati da ke ƙasar nan ba su shiguwa a wajen naƙasassu sannan yawancin su su na buƙatar wasu na’urori da hanyoyin kimiyya da fasaha da za su taimake su wajen samun ilimi da koyo a cikin sauƙi.

Ta ce, “Akwai buƙatar a fito da hanyoyin da za su rage rainin da ake yi wa mutane masu naƙasa ta hanyar fito da babban gangamin faɗakar da jama’a, tare da cire duk wasu nau’o’i na nuna wariya da kuma inganta hanyoyin su na samun abinci. 


“Akwai buƙatar a samu cikakkun bayanai game da naƙasassu, sannan bada satifiket ɗin naƙasassu ya na da muhimmanci wajen tabbatar da cewa su na cin moriyar wannan hukumar don a kauce wa cutar da wasu za su iya yi a aikin kyautatawar da gwamnati za ta riƙa yi.”


Har ila yau ministar ta bayyana cewa ta bai wa naƙasassu kayayyakin agaji don tabbatar da cewa su ma sun amfana da ayyukan da ma’aikatar ta ke yi da kuma dukkan shirye-shiryen inganta rayuwa.


Ta ce, “A yau dubban naƙasassu an taimaka masu kai-tsaye ta hanyar shirye-shiryen mu daban-daban.”

Hajiya Sadiya ta yi kira ga gwamnati da ta ci gaba da bada goyon baya don tabbatar da cewa an kyautata rayuwar dukkan naƙasassu da ke Nijeriya.


A jawabin da ya mayar, Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙalubalanci Hukumar Naƙasassu ta Ƙasa da ta yi aikin ta sosai wajen ganin an cimma ƙudirin gwamnati na ceto ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga ƙangin fatara da yunwa.


Ya ce, “Ba a yi kuskure ba wajen naɗa ku da aka yi domin kuwa  dukkan ku an zaɓo ku ne bayan an yi nazari sosai kan halayen ku da kuma gudunmawar da ku ke bayarwa ga al’umma da kuma naƙasassun da ke Nijeriya.


“Aikin da ke gaban ku babba ne. Tilas ne ku yi aiki tuƙuru domin tabbatar da cewa gwamnati ta samu nasarar inganta rayuwar ‘yan’uwan ku masu buƙatu na musamman duk da rashin isassun kuɗi da mu ke fama da shi.” 

Shugaban ya bada tabbacin cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da bada goyon baya ga duk wasu yarjejeniyoyi da ke kare haƙƙin mutane masu naƙasa.


Ya ce, “Nijeriya ta na cikin ƙasashen da su ka rattaba hannu kan Ƙudirin Majalisar Ɗinkin Duniya kan Mutane Masu Naƙasa wadda ke neman ganin an kare haƙƙin naƙasassu a dukkan wani shiri na kawo cigaba a duk duniya.


“A ƙarƙashin shugabanci na, gwamnati za ta ci gaba da goyon bayan duk wasu yarjejeniyoyi da aka yi na duniya da yanki ko sashen ƙasa da ƙasa waɗanda ke neman inganta rayuwar ‘yan’uwan mu masu buƙatu na musamman.”


Tun da fari dai sai da Majalisar Dattawa ta gama aikin tantance tare da amincewa da naɗin Hon. Dakta Husseini Hassan Kangiwa daga yankin Arewa Maso Yamma a matsayin Shugaban Hukumar Naƙasassu ta Ƙasa kamar yadda Sashe na 32(3) da na 40(1) na Dokar Hana Wariya Ga Naƙasassu ta 2019 ta tanadar. 

Sauran membobin hukumar su ne:


Mrs. Esther Andrew Anwu, Memba daga Arewa ta Tsakiya


Malam Abba Audu, Memba daga Arewa ta Gabas


Malama Amina Rahma Audu, Memba daga Arewa ta Yamma

Mista Jaja Oparaku, Memba daga Kudu Maso Gabas 


Ms. Philomena I Konwea, Memba daga Kudu Maso Kudu


Mista Omopariola Busuyi,Memba daga Kudu Maso Yamma


Mista James David Lalu, Babban Sakatare, daga Arewa ta Tsakiya

Loading

Previous Post

Yadda ‘yan dawunlodin ke kassara finafinan Hausa a YouTube

Next Post

Fatawar saki a fim: Shugabannin Kannywood sun yi wa Sheikh Bashir Alfurƙan tambihi

Related Posts

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Next Post
Fatawar saki a fim: Shugabannin Kannywood sun yi wa Sheikh Bashir Alfurƙan tambihi

Fatawar saki a fim: Shugabannin Kannywood sun yi wa Sheikh Bashir Alfurƙan tambihi

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!